Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Murtala Nyako Yace Ana Neman Karar da 'Yan Arewa


Gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako.
Gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako.

Gwamnan na Adamawa yace gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan ta kulla yakin kawar da 'yan arewa ta hanyar kisa, cin zarafi da yin ko oho da batun tsaron dake addabar yankin.

Gwamna Murtala Nyako na Jihar Adamawa, ya zaegi gwamnatin PDP ta shugaba Goodluck Jonathan da laifin yakin kawar da 'yan arewacin Najeriya ta hanyar kisan gilla, cin zarafi da kuma yin banza da matsalolin tsaron dake wakana a yankin.

A cikin wata takartdar da ya aikewa da kungiyar gwamnonin arewacin Najeriya, gwamnan na Adamawa yace lallai akwai abin dubawa a game da wasu abubuwan da suka faru cikin 'yan kwanakin nan, kama daga harin bam na Abuja da sace yara mata 'yan makaranta a Chibok, Jihar Borno, da ma kashe kashe ko yunkurin kashe sarakuna, malamai, shugabannin addini da na siyasa ciki har da shugaban majalisar dattijai da shi kansa gwamnan na Adamawa.

Darektan yada labarai na gwamna Nyako, Mohammad Sajo, yace gwamnan na Adamawa ya rubutawa 'yan'uwansa gwamnonin arewa wannan tajkarda ce domin janyio hankulansu ga wadannan abubuwa da ake dauka tamkar matsaka ta yankin arewa maso gabashin Najeriya, wadda kuma take iya zama matsalar arewa baki daya tare da Najeriya.

Yace abu na biyu da gwamna Nyako yake fadakarwa a kai shi ne cewa irin kashe-kashen da ake yi a kasar nan sun kai matsayin da za a iya bayyana su a zaman kisan gilla ko na neman kare-dangi, kuma wadanda aka damkawa alhakin tsaro ba su yin wani abu na kawo karshen wannan zub da jinin dake bazuwa tare da neman lakume ko ina da kowa.

Wani mai fashin baki, Mr. Mohammed Isma'il, yace akwai abin dubawa game da kalamun gwamnan.

Yace gwamna Nyako yana matsayin da zai iya saninw adannan abubuwan da yayi magana a kansu, kuma duk alamun da ake gani, kama da yadda muggan makamai ke shiga hannun 'yan Boko Haram, duk sun nemi gaskata kalamun gwamnan.

Har yanzu ba a ji ta bakin gwamnatin tarayya kan wadannan kalamu na gwamna Murtala Nyako ba.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG