“(Nyako) yayi wasu tambayoyi wadanda har yau, har gobe gwamnatin Tarayya bata iya bada amsa ba. Maimako, sai suka koma zaginshi. Sun kasa bada amsa, kuma suna zaginshi, shine ya mayarda Nyako gwarzo, saboda babu irinshi a cikin gwamnoni.”
Barrista Dalung ya cigaba da cewa “Nyako gwarzo ne wanda baza a iya hada shi da wani irin gwamna ba, domin a matsayinshi na gwamna, yayi banza da kowani irin dadi, ya fita ya fadi gaskiya. Bai damu ko za’a hallaka shi ba. Bai damu ko zai rasa ranshi ba.”
Barrista Dalung ya soki lamirin gwamnonin da suka soki Nyako.
“Martanin da wasu gwamnoni suke mayarwa, irin kukannan ne, da kare yake yi idan yaga kura ta wuce, saboda ba zai iya kaiwa kura hari ba. Idan su maza ne, abubuwan da yake faruwa”, Barrista Dalung ya kammala.
A halin yanzu dai gwamnatin tarayya ta rage yawan jami’an tsaro dake gadin gwamnan Jihar Adamawan daga 120 zuwa 30 kacal, wanda kawo yanzu babu cikakken bayani daga hukumomin abinda ya shafa, yayin da jiragen sama masu saukar ungulu na soji ke cigaba da shawagi.