A wata takarda da aka rabawa manema labarai, wanda Muryar Amurka ya samu a Damaturu, dake dauke da sa hannun Abdullahi Bego, mai baiwa gwamna Geidam shawara akan harkokin yada labarai, da Ahmed Sajo, darektan yada labarai na gwamna Nyako.
Gwamnonin biyu sun nuna takaicinsu akan furucin Clark, inda suka ce hakan yayi nuni karara akwai jahilci akan kundun tsarin mulkin Najeriya.
Samun takardar ke da wuya, wakiliyar Muryar Amurka Sa’adatu Fawu ta tuntubi Abdullahi Bego, mai baiwa gwamna Geidam shawara a gidan gwamnatin Jihar Yobe, domin jin karin bayani.
“To wannan kasida da muka rabawa manema labarai, martani ne akan wasu kalamai na rashin kan gado, da kuma makarkashiya da wani tsoho da ake kira Edwin Clerk yayi”, a cewar Mr. Bego.
Abdullahi Bego ya cigaba da cewa “shi Edwin Clerk bana bukatar na gabatar da shi. Kowa ya san shi yana ikirarin shi maigidan shugaban Najeriya ne.”
“Yayi kira ga shugaba Jonathan akan ya kawar da gwamnonin Borno da Yobe da Adamawa daga kan mukamansu na gwamna, ya nada kantomomi na soja saboda wannan yanayi na tabarbarewar tsaro, da muke ciki. Saboda haka muka fitar da wannan kasida, muka ce wannan bayani ne mara kan gado, na mutumin da bai san me ake ciki ba, ko kuma ya sani, amma kuma yana so ya janye hankulan jama’a daga ainihin hakikanin abunda yake faruwa,” inji Abdullahi Bego.
Yanzu dai misalin shekara daya kennan da kafa dokar-ta-baci a jihohin Yobe, Borno da Adamawa, jihohi uku dake fama da ta’addanci.
A kwanakin baya gwamnan Jihar ta Adamawa, daya daga cikin jihohi uku dake da dokar-ta-baci, Nyako ya dauki alwashin tattara takardun shaidu domin kai karar shugaban Najeriya a kotun bin kadin manyan laifuka ta kasa da kasa, wato ICC a takaice dake can birnin Hague a Netherlands, akan abunda ya kira kisan kare dangi akan mutanen arewacin Najeriya.
A halin yanzu dai gwamnatin tarayya ta rage yawan jami’an tsaro dake gadin gwamnan Jihar Adamawan daga 120 zuwa 30 kacal, wanda kawo yanzu babu cikakken bayani daga hukumomin abinda ya shafa.
A kwanakin baya, 'yan siyasa sun bayanna cewa Shugaba Jonathan na so ya sabonta dokar-ta-baci, amma 'yan majalisar na daura dammarar adawa da hakan.