Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nyako Yaki Janye Kalamansa


Admiral Murtala Nyako mai ritaya, gwamnan Jihar Adamawa.
Admiral Murtala Nyako mai ritaya, gwamnan Jihar Adamawa.

Gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako yace bashi da wata nadama kan abunda ya fada na zargin shugaban Najeriya Jonathan da yiwa jama’ar arewacin Najeriya kisan kiyashi, duk da sukan da wasu suke mishi.

A taron shuwagabanni da aka gudanar a karshen makonnan a birnin Tarayya Abuja, masu fada a ji, kamar gwamnan jihar Neja Mu’azu Babangida Aliyu da wasu shuwagabanni sun soki kalaman Admiral Nyako mai ritaya, inda suka nemi jama’a suyi watsi da su, suna masu cewa kazafce-kazafcen gwamnan na jihar Adamawa basu da tushe balle makama.

Murtala Nyako yayi magana ne ta bakin kakakinsa Ahmed Sajo, wanda yace “Ina so in shaida maka cewa rahoto da ake fada na caccaka, ina ganin an fade shi ne dai kawai saboda wata kila a farantawa wasu rai, amma alal hakika, a duk taronnan da akayi babu wanda ya karyata kalma daya wanda gwamna Murtala Nyako ya fadi.”

Ahmed Sajo yayi bayanin abubuwa uku da sauran takwarorin Nyakon suka fada a wajen taron, dangane da kalaman gwamnan.

“Abu na farko suka ce maganar da yayi zai kawo rabuwar kawuna a kasa. Abu na biyu, suka ce maganar da yayi zata baiwa ‘yan bindiga karfin gwiwa. Abu na uku suka ce wanda zai yi irin wannan kalami ya tabbata yana da hujja mai kwari”, a cewar Mr. Sajo.

Wakilin Murtala Nyako ya mayar da martani akan wadannan abubuwa guda uku.

“Na farko dai, idan akwai abunda ya kawo rabuwar kawuna, babu abinda yafi ana kisa a kasa, babu wanda yake magana. Kowa idan yayi gefe zai yi magana a boye, amma a bayyane kowa yana shakkar fadin gaskiyar abunda ke faruwa. Wannan kashe-kashe da akeyi hakika ba hairan bane, kuma babu wanda yake bukatarsa,” inji Ahmed Sajo.

Sajo ya cigaba da cewa “Na biyu, batun cewar ana karawa wasu karfin gwiwa wannan ba gaskiya bace, gaskiya itace idan akwai inda aka samu gazawa a wurin wanda yake da hakkin dakatar da wannan abun, a gaya masa an samu gazawa, shine an karawa masu wannan harkar karfin gwiwa. Amma idan aka ce ga gazawa a boye ta kar a fade ta, saboda gudun kar wani ya zargi wani, to wannan abun mu muna gani shi zai kara musu karfin gwiwa fiye da yadda ake tsammani”

“Abu na uku, cewa wanda zai yi magana ya tabbata yana da hujja mai karfi, alal hakika basu ce hujjar Murtala Nyako bata da kyau ba, kawai cewa suka yi mai magana yayi amfani da hujja. Sun tambaye shi hujjarshi, kuma ya gaya musu”, Ahmed Sajo ya kammala bada bayanansu guda uku.

Aliyu Mustaphan Sokoto na Sashen Hausa ya tambayi mai baiwa gwamnan jihar Adamawan shawara, ko meyasa gwamnan jihar Neja, Muazu Babangida da Labaran Maku da Kanal Dangiwa suka yiwa Nyakon caa suna sukan lamirinshi, cewa maganganun da yake yi suna iya janyo tashin hankali a kasa.

Ahmed Sajo ya bada amsa “wadannan ka san, wadansunsu sun riga sun rabu da talakawansu da dadewa. Mutumin da yake zaune a gidansa, yake cin abinci da jama’arsa da talakawansa, yake sauraron abunda talakawansa ke fada, yana iya fadan ra’ayin da yayi dai-dai dana talakawansa. Mutumin da kuma yake gidan gwamnati, ko wani gida wanda akwai tsaro, ba’a bari jama’a suje wajensa bai san me jama’a ke ciki ba. Shi kuwa baya muamala da jama’a. Murtala Nyako alhamdulilLahi, yana mu’amala da talakawansa, yana nan a gidansa yadda jama’a ke zuwa wurinsa kafin ya zama gwamna, haka suke zuwa wurinsa a yanzu haka ma. Ya san abunda ke faruwa.”

Jihar Adamawa da Murtala Nyako yake shugabanci na daya daga cikin jihohi uku dake da dokar-ta-baci, wanda a cikin kalaman gwamna Nyako yake cewa Bom bai taba tashi a jihar ba, amma an saka mata dokar-ta-baci, idan aka kwatanta da birnin tarayya Abuja inda boma-bomai suka tashi, amma babu dokar-ta-baci.

Gwamnan wanda tsohon hafsin sojin ruwa ne, ya dauki alwashin tattara takardu masu dauke da shaidun kisan kiyashi domin kai karar shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a gaban kotun bin kadin manyan laifuka ta kasa da kasa.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG