Sun shirya gangamin ne domin karbar Atiku Abubakar tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya wanda ya yiwa jam'iyyarsa ta PDP adabo ya koma APC. Yayin gagamin tsohon gwamnan Bayelsa Mr. Da Silva ya mika neman gafarar al'ummar Neja Delta bisa abun da ya kira kasawar da dansu ya yi. Ya ce a shekarar 2011 ya ziyarcesu tare da wasu gwamnoni arewa inda suka amince su zabi shugaba Goodluck Jonathan kuma suka yi hakan. Amma gashi ya kasa yin komi. Ya ce don haka al'ummar Neja Delta ta umuarceshi ya zo ya nemi gafararsu kuma ya tabbatar masu cewa zasu yi aiki da 'yan arewa a sabuwar jam'iyyar APC domin kawo canji da cigaban kasa.
Shi ma Atiku Abubakar ya yi karin haske game da dalilan da suka sa ya bar PDP. Ya ce na daya zasu kafa kwamitin riko na jam'iyyar. Na biyu su tabbatar cewa ranar Laraba wato gobe sun fito an yi masu ragista. Ya ce basu fara kemfen ba. Idan sun fara zasu ji jawabi daga wurinsa. Ya ce canji na zuwa kuma sai an yi canjin a Najeriya.
Gwamnan Adamawa Murtala Nyako ya ce yanzu an bude wani sabon babi a faggen siyasar jihar da na kasa. Idan Allah ya yarda zasu dakatar da zaluncin da a keyi a Abuja.
Amma Barrister A. T. Shehu sakataren jam'iyyar PDP a jihar Adamawa ya ce su basu damu da gangamin ba ko kuma ficewar Atiku Abubakar. Ya ce siyasa ta gaji shigowa da ficewa. Domin wani ya fita ko ya shigo ba zai sa ka ci zabe ba ko ka fadi zabe ba.