Ana Tsaftace Yankunan Da Mahaukaciyar Guguwa Ta Ratsa A California 

California

Bayan wata mahaukaciyar guguwar da ta yi kaca-kaca da wasu yankunan California a Amurka, ana ta yunkurin shara tare da gyara barnar da ta yi a ranar Laraba, yayin da aka samu saukin saukar ruwan sama a yankuna da dama.

WASHINGTON, D.C. - Ko da yake, ana sa ran arewacin kasar na iya fuskantar wani yanayi mai tsananin nan da zuwa ranar Juma’a.

Akalla mutum 17 ne suka mutu sakamakon guguwar da ta afkawa jihar. Mai yiyuwa ne adadin ya karu, in ji Gwamna Gavin Newsom yayin wata ziyara da ya kai a birnin Capitola da ke gabar tekun Santa Cruz.

Fiye da rabin kananan hukumomi 58 na California an ayyanasu a yankunan da bala'i ya afkawa, in ji gwamnan.

Ma’aikatan sun ta aikin sake bude wasu manyan titunan da duwatsu suka rufe, da ambaliya ko kuma laka ta rutsa da su yayin da sama da mutum 10,000 da aka ba su umarnin ficewa daga garuruwan da ke gabar tekun da ke tsakiyar gabar teku aka bar su su koma gida.

-AP