Sanatar California, mai shekaru 56, ita ce mace bakar fata ta farko kuma mai dangantaka da Kudancin Asiya da aka zaba a matsayin Mataimakiyar Shugaban kasa. Tana wakiltar al'umma masu mabanbantan al’adu da aka san Amurka da shi, wanda kuma babu su a cikin gwamnatin tarayyar a Wshington. Matsayinta na bakar fata ya bata damar furta albarkacin bakinta game da zaluncin ‘yan sanda da wari da wariyar launin fata.
Harris ta kasance jaruma a siyasar dimokradiyya a cikin shekaru 20 da suka gabata, inda ta rike mukamin lauyar gunduma a San Francisco da babbar Lauya ta jihar California kafin ta zama sanata. Bayan ta kammala takarar neman zabe na Shugaban Kasa a karkashin jam’iyyar Democrat, sai Biden ya zakulo ta ta mara masa baya a matsayin Mataimakiyar Shugaban kasa. Za a rantsar da su a matsayin Shugaba da Mataimakiyar Shugaban Kasa ranar 20 ga watan Janairu.
Zaben nata da Biden yayi, na da matukar muhimmaci saboda zai kasance Shugaban kasa mai yawan shekaru da za a rantsar, shekaru 78, kuma bai yi alkawarin neman wa’adi na biyu ba a shekara ta 2024.
Harris kullun na ganin nasararta a matsayin gado da zata bari a tsakanin mata bakar fata da suka yi takara kafin ita, kamar su Mary McLeod Bethune da yar rajin kare hakki Fannie Lou Hamer da Shirley Chrisholm bakar fata ta farko da ta tsaya takarar Shugaban Kasa a shekarar 1972.
“Ba a gaya mana labarinsu a koda yaushe,” inji Harris a watan Agusta locacin da aka zabe ta ta tsaya Mataimakiyar Shugaban Kasa a jam’iyyarta. “amma a matsayinmu na Amurkawa, dukkan mu muna tsaye akan kafadunsu.”
Tarihin yana zuciyar Sara Twyman baya bayan nan locacin da take kallon kamfe din Harris a Las Vegas kuma take sanye da riga dauke da sunanta jere da na Chisholm.
“Locaci yayi da mace zata dare mukami mafi girma a gwamnatinmu,” inji Twyman 'yar shekara 35 kuma bakar fata.
Duk da farin cikin da ke kewaye da Harris, ita da Biden suna fuskantar kalubale masu yawan gaske, ciki har da tsanantar karuwar wariyar launin fata a Amurka, a yayin annoba wanda yafi tsananta a tsakanin wadanda ba farar fata ba da kuma jerin kashe-kashen bakar fata Amurkawa. Ayyukan da Harris tayi a baya a matsayinta na mai gabatar da kara, ya haifar da shakku a tsakanin masu ra’ayin ci gaba da matasa masu kada kuri’a wadanda suke kallonta a matsayin wacce zata sa a sake fasalin aikin ‘yan sanda da tsarin magunguna da sauransu.
Jessica Bryrd, wacce ta jagoranci wani shirin na samar wa bakar fata adalci a kan zabuka da ake kira Movement for Black Lives’ electoral Justice Project and Frontline, kungiyar hadakar al'adu masu yawa da suka hada karfi wajen zaburar da masu kada kuri’a, tace tana bullowa da shirye shiryen da za su tsara ayyuka, wanda hakan kuma zai saita Harris da Biden akan turbar tsare tsare na ci gaba.
“Nayi Imani da kwazon shugabancin mata bakar fata, ko duk siyasunmu basu dace da juna ba.” Inji Byrd. Ina so mu jajirce akan cewa wakilci abun murna ne, ya dace muyi farin ciki kuma muna da mata bakaken fata da suka cancanci a daga su.”
Harris itace mace ta biyu bakar fata da aka zaba a matsayin Sanata. Abokan aikinta, Sanata Cory Booker itama bakar fata, tace zamanta a majalisar ya maida wurin inda “jama’a ke iya kai wa” ta kuma yi alkawarin mai da ofishinta na Mataimakiyar Shigaban Kasar haka.
An haifi Harris ne a shekarar 1964 kuma iyayenta jajirtattun masu rajin kare hakki ne. Shymala Gopalan daga Indiya da Donald Harris daga Jamaika sun hadu ne a Jami’ar California dake Berkely, a 1960, locacin yana gidan ‘yan zafin kai game da rajin kare hakki. Sun rabu bayan Harris da ‘yar uwarta sun zama ‘yanmata kamu Harris ta girma a hannun mahaifiyarta wacce ta rasu kuma Harris ta bayyanta a matsayin wacce ta taka muhimmiyar rawa a rayuwarta.
Kamala suna ne da aka samu daga “furen Lotus” kuma Harris ta girmama tushenta na Indiya a yayin kamfe dinta, ciki har da kira ga “Chittis” Kalmar dake nufin Gwaggon ta ta wajen uwa da harshen Tamil a locacin bayaninta na farko a matsayin mai marawa Biden baya.
Zolaya da ‘yan Republican suke mata saboda sunanta ciki har da Trump na daga cikin kalubale data fuskanta. Trump da ‘yan barandansa, sunso suyi mata lamba da cewa mai tsatstsaurar ra’ayi ce duk da irin tarihinta na sassauci, wani yunkuri na nesanta ta daga jama’a da nuni da yadda shugabancin mace bakar fata zai kasance.
‘yar majalisa Pramila Jayapal ta Washington tace karfin Harris ba daga ayyukanta na rayuwa bane kawai, yana kuma daga jama’ar da take wakilta. California na matsayin jiha mafi yawan jama’a kuma nada al’adu da yawa mai kusan kaso 40 cikin dari na Latino da kaso 15 kuma ‘yan Asiya. A majalisa, Harris da Jayapal sun hada kai suna tura kuduri na ganin sun sama wa Musulmi wakilci wadanda Trump ya kakaba wa takunkumin tafiye tafiye a 2017 da kuma neman fadada damar daukan hadimai a gidaje.
“Wadannan sune irin tsare tsaren da suke iya samuwa idan kuna da wakilci irin namu,” inji Jayapal wacce ta lashe zabe a matsayin mace ta farko ‘yar Kudancin Asiya da aka zaba a majalisar Amurka.
Mahaifiyar Harris ta rainesu da zummar duniya zata kallesu a matsayin bakar fata, a cewar Harris, kuma haka take gabatar da kanta a yau.
Tayi karatu a Jami’ar Howard, daya daga cikin Jami’oin a cikin tarihi da suke na bakake kuma dake dauke da kungiyar mata bakar fata dake da alkawarin Alpha Kappa Alpha. Ta sha gabatar da Kamfe dinta a HBCU kuma takan yi kokarin magance matsalolin matasa bakar fata maza da mata tare da kudurin kawar da wariyar launin fata.
Nasararta na iya zai janyo mata da maza bakar fata zuwa siyasa.
Magajiyar garin San Fransisco, London Breed, wadda ta ke daukar Harris a matsayin malamarta, a bar koyi, ta ce:
“Amurkawa ‘yan Afrika har yanzu basu rabu da tunanin harkar bauta ba da kuncin wariyar launin fata a wannan kasar, har yanzu muna jin zafin abun da yadda aka wulakantamu da abun da ya faru na wariyar launin fata,” Inji ta. Mukamin Harris “ya daukakemu kuma ya daga darajarmu ya sa mu cikin farin ciki game da abunda ka iya faruwa.”
Harris na auren Bayahude ne Doug Emhoff, wanda ‘ya’yansa na wata matar na ce mata “Momala.” Farin cikin game da mukamin nata ya ratsa mata na wasu kabilu.
Kawayenta Sarah Lane da Kelli Hogde tare da ‘ya’yansu uku, yan mata shida sun halarci gangamin zaben Harris a Phoenix a ranar rufewa. “ Wata mota ta cika da ‘yan mata kanana wadanda suke dauka da fata mai girma, "Ci gaba Kamala!” shi ne sakon wani rubutu da aka lika a jikin motar.
Lane, ‘yar shekaru 41 mai shari’a ‘yar kabilar Sfaniya ce kuma tana da ruwan Asiya, ta tallafa wa Biden da Harris a karon farko data taba aikin kamfe. Da aka tambaye ta dalilin kawo ‘ya’yanta ‘yan shekara 6 da 9 da 11 su ga Harris, sai tace,”Ina son ‘yan matan su ga abunda mace zata iya yi.”