Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Mika Mulki Na Biden Ya Kama Aiki Gadan Gadan


Joe Biden
Joe Biden

Kwamitin mika Mulki na Joe Biden bai jira sanarwar sakamakon zaben shugaban kasa ba ya kama aiki gadan gadan.

Kwamitin mika Mulki na Joe Biden bai jira sanarwar sakamakon zaben Shugaban kasa ba ya kama aiki gadan gadan.

Tun kafin nasarar ta Biden ta ranar Asabar, dadadden hadiminsa Ted Kaufman yana kan gaba wajen tabbatar da ganin cewa tsohon mataimakin shugaban kasa zai fara aikin kafa gwamnati gabannin nasarar zaben.

Kaufman tsohon sanatan Delaware ne wanda aka zaba ya maye gurbin Biden locacin da ya zama mataimakin shugaban kasa.

Da farko Biden gaya ma Kaufman ya fara aiki a kwamitin kila -wa -kala tun a watan Afirilu jim kadan da tsohon mataimakin shugaban kasan ya samu tikitin zama dan takarar jam'iyyar Democrat a karshen zaben fitar da dan takara na jam'iyyar Democrat.

Shirin mika mulki na iya zama abin da ake yi cikin zakuwa ko a yanayi irin na yau da kullum.

Wannan al'amari yayi kama da na takarar shugaban kasa na shekarar 2000 da kuma tashin hankalin da aka gani na sake kirgen kuri’un Florida. Bayan sama da wata guda rigima tsakanin dan takarar Republican Goerge W. Bush da dan Democrat Al Gore wanda kotun koli ce ta raba gardamar, wanda kuma wannan rigimar ta kasara wa’adin kwamitin mika mulki zuwa kwanaki 39 kafin rantsar da shugaban a watan Janairun 2001.

Clay Johnson, wanda ya shugabanci kwamitin mika mulki ga Bush ya ce, mashawartan Biden sun kasa "jira su tabbatar da cewa shugaban kasan da aka zaba lallai shine shugaban da aka zaba.".

Johnson yace, a watan Yunin 1999, kusan watanni 17 kafin ranar zabe na shekara ta 2000, Bush ya same shi da zancen shugabancin kwamitin ganin mahaifinshi ya shiga irin wannan al'amarin shekaru 11 da suka wuce. Kafin ranar zaben Bush ya riga ya zabi Andy a matsayin shugaban ma’aikata na kwamitin da kuma na fadar White House.

Johnson yana ganin sunyi riga malam masalaci. Sai kuma ga zancen sake kidaya ya taso.

Bayan wajen kwanaki 10 na farko sai mataimakin Bush, Dick Cheney ya fada wa Johnson da ya fara tara kudi da yanke shawara kan irin ma'aikatan da zai bukace su, tare da bayyana cewa za a warware matsalar ko ta wane hali.

Tawagar Bush ta kasa gudanar da binciken da hukumar FBI ka yi akan wadanda ake sa ran zasu kasance masu mukamai da sauransu, gabannin sanar da wanda ya lashe zabe. A maimakon haka sai suka yi amfani da tsohon lauyan fadar White House, a lokacin gwamnatin Reagan ya gudanar da tantancewa kan duk wata matsalar da ka taso dangane da yanayin rayuwar wadanda za a nada.

“Ya kamata suyi tunanin kune din, amma kar ku wuce gona da iri, amma ya kamata kuyi aiki tukuru kamar kune din,” Johnson ya fada wa tawagar Biden. “ya kamata da kun fara yin hakan tun ranar Talata da dare.”

Kwamitin kamfe din Biden ya ki yayi magana game da matakan kwamitin mika mulkin. Mafiya kusa da shi daga cikin masu ba shi shawara, sun ce abu mafi muhimmanci shi ne sanar da shugaban ma’aikata na fadar White House sai kuma tattara bayanai da ake bukata don magance coronavirus.

Shugaban Kasa yakan samu mukamai da zai nada dubu 4,000, kuma fiye da dubu 1,200 daga ciki sai Majalisar Dattawa ta amince da su. Wannan zai iya zama kalubale ga Biden saboda Sanatocin Republican sun fi rinjaye.

A hukumance matakan mika mulki kan fara ne da zarar hukumar gudanarwa ta tantance wanda ya ci bisa dukkan bayanai. Wannan tsarin bai da takamaiman hurumi don haka Trump zai iya tursasa darektan hukumar ya tsaida komai.

It's also unclear if the president would meet personally with Biden. Obama met with Trump less than a week after the election, but there was no dispute about him having topped Hillary Clinton in the Electoral College.

Babu bayani kan ko shin shugaba Trump shi kansa zai gana da Biden. Obama ya gana da Trump ‘yan kwanaki bayan zaben, amma a lokacin babu wata takaddama bayan da shi ya kada Hillary Clinton a zabe na cin kason kuri'u (wato electoral college, a Turance).

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG