Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Halin Da Ake Ciki Yayin Da Biden Ya Shige Trump a Pennsylvania


Trump a hagu, Biden da dama
Trump a hagu, Biden da dama

Dan takarar jam’iyyar Democrat Joe Biden ya kara kusantar yiwuwar samun nasarar lashe zaben shugaban Amurka yayin da alkaluman da aka sabunta suka nuna ya tserewa Shugaba Donald Trump a jihohin Georgia da Pennsylvania.

Yanzu haka Biden na gaba a yawan kuri’un da aka kada a duk fadin kasar da kuma yawan kuri’un kwalejin masu zabe da kuri’u 253 yayin da Biden ke da 214 – inda ake bukatar dan takara ya samu rinjaye da kuri’a 270 kafin ya samu wa’adin mulki na tsawon shekara hudu a matsayin shugabvan kasa.

Har yanzu ana ci gaba da kidaya kuri’u a wasu jihohi hudu wadanda su za su tantance wanda ya yi nasara – wato jihohin Arizona da Nevada, wadanda Biden ke gaba

Da safiyar ranar Juma’a Biden ya wuce Trump da yawan kuri’u yayin da ya yi masa fintinkau da kuri’a 917 a Georgia.

Amurka na amfani ne da tsarin zaben “Electoral College,” wanda ke ba dan takara dama ya samu, idan ya lashe kuri’un kowacce jiha – ban da jihohin Maine da Nebraska.

Kuri’un na kwalejin masu zabe ko “Electoral College,” ana raba su ne bisa iya adadin al’umar kowacce jiha.

Ba tare da wata hujja ba, a ranar Alhamis shugaba Trump ya zargi ‘yan Democrat da yunkurin tafka magudi domin su hana shi samun wa’adi na biyu.

“Wannan al’amari ne na yunkurin sace wannan zabe, suna so su tafka magudi,” in ji Trump yayin wani taron manema labarai.

Sabanin hakan, a wannan rana, Biden ya yi kiran a kara hakuri yayin da jihohi ke ci gaba da tattara alkaluman zaben, wanda sama da mutum miliyan 150 suka kada kuri’unsu a wannan shekara.

“Wajibi ne a kirga kowacce kuri’a. Kuma abin da za mu tabbata ana ci gaba da yi kenan. Kuma haka ya kamata a yi. Shi tsarin dimokradiyya, haka yake zuwa da rudani a wasu lokuta.” Biden ya ce.

Kirgan Kuri’u

Trump na bukatar ya ci gaba da rike dukkan jihohin da yake gaba da yawan kuri’u sannan ya lashe Nevada da Arizona, wadanda a halin da ake ciki, duka Biden ne ke kan gaba.

Sakatariyar jihar Pennsylvania, Kathy Bookkvar ta fada a ranar Alhamis cewa, kusan ilahirin kuri’un da ba a kirga ba, wadanda aka kada su ne ta hanyar gidan waya.

Kuma a halin da ake ciki Biden ne ya lashe su.

Inda ake kidaya kuri'a a Amurka
Inda ake kidaya kuri'a a Amurka

Gangamin yakin neman zaben Biden ya yi kira ga magaoya bayansa da su yi amfani da gidan waya wajen kada kuri’unsu domin kaucewa cutar coronavirus, yayin da Trump wanda ba tare da ya gabatar da wata hujja ba, ya ce hakan zai ba da kofar yin magudi.

Shugaba Trump ya yi nuni da kuri’un da suka zo daga baya-baya wadanda Biden ya lashe a matsayin wadanda y ace mai yiwuwa an hada baki ne da gwamnonin jihohin da ‘yan Democrat ke mulki aka kada su.

“Muna samun nasara a duk muhimman wurare da kuri’u da dama, kwatsam sai kuma alkalumanmu suka fara raguwa a boye,” Trump ya fada a ranar Alhamis.

Ita dai jihar Pennsylvania na da kuri’u 20. Trump dai yana da kwakkwarar madafa a jihohi biyu wadanda ba a bayyana alkalumansu ba, wato Alaska da North Carolina.

Da safiyar yau Juma’a, Biden yana gaba da kuri’a 11,500 a Nevada, wacce ke da masu masu zaben kwaleji shida sannan yana gaba a Arizona da kuri’a 47,000, wacce ke da kuri’a 11.

Akwai dai kuri’u da dama da ba a kirga a wadannan jihohi biyu ba.

A daukacin kuri’un gama-gari da aka kada, Biden ke ba da kuri’a miliyan 73.5 yayin da Trump ke da miliyan 69.5, sai dai tsarin zaben kwaleji ne zai fayyace wanda zai lashe wannan zabe da aka kwashe watanni ana zazzafan kamfe.

Shi dai Trump ya shiga shafin Twitter ya nemi a dakatar da kidayar da ake yi.

Sai dai idan aka dakatar da kidayar a yadda take a daren Alhamis, Trump zai fadi zaben – hakan zai sa ya zama shugaban A murka na uku da zai sha kaye wajen neman wa’adi na biyu cikin gomman shekaru hudu da suka gabata.

Garzayawa Kotu

A ranar Alhamis, Trump ya yi ikrarin an tafka magudi, inda ya ce jami’an zabe a wasu jihohi sun hana wakilian gangamin yakin neman zabensa su saka ido kan kidayar, yana mai ayyana tsarin yin zabe ta gidan waya a matsayin “gurbataccen tsari” da ba shi da “hanyoyin tantancewa.”

Trump ya ce yana sa ran za a tafka shari’ar da za ta kare a kotun kolin kasar.

Lauyoyin da wakiltar Trump da jam’iyyar Republican, sun shigar da kara suna masu ikrarin cewa an tafka magudin zabe tare da neman a dakatar da kirga kuri’un Pennsylvania.

Ginin Kotun Kolin Amurka
Ginin Kotun Kolin Amurka

Aikin kidaya kuri’un a sassan Amurka, ya fuskanci jinkiri sanadiyyar dumbin kuri’u da aka kada ta gidan waya – wadanda adadinsu ya kai kashi biyu cikin uku na sama da kuri’a miliyan 101 da aka jefa gabanin ranar Talata da aka yi zaben a hukumance.

Da yawa daga cikin wadanda suka aika kuri’unsu ta gidan waya, sun ce sun yi hakan ne don kaucewa dogayen layukan zabe da kuma yin gaba da gaba da jama’a saboda annobar coronavirus da aka kasa shawo kanta.

Shi dai gangamin yakin neman zaben Biden ya goyi bayan kada kuri’a ta gidan waya, kuma sakamakon hakan ya sa adadin kuri’un da yake samu suka karu a jihohi yayin da ake tattara alkaluma.

Ana shi bangaren, Trump ya nemi magoya Republican ne su je rumfunan zabe su kada kuri’unsu da kansu, yana mai cewa za a tafka magudi idan aka yi zaben ta gidan waya, ba tare da ya kafa wata hujja ba. Wadannan kuri’u an riga an kidaya su.

Lauyoyin Trump sun kuma yi kira da a sake kidaya kuri’un jihar Winsconsin da ke tsakiyar yammacin Amurka, inda a ranar Laraba aka yi hasashen Biden ne zai lashe jihar mai wakilai 10.

Sun yi ikrarin cewa, an tafka magudi a wasu rumfunan zabe.

Da safiyar ranar Laraba Trump ya yi ikrarin shi ya lashe zabe, amma Biden ya yi akasin hakan.

“Ba na zo nan da na fada muku cewa na lashe zaben ba ne,” in ji Biden a ranar Laraba. “Amma na zo ne don fada muku cewa, idan aka kammala kidayar, mun yi imanin cewa za mu samu nasara.”

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG