Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Ana Cigaba Da Dakon Sakamakon Zaben Amurka


'Yan takarar shugabancin Amurka duka biyu, kowannensu na ikirarin shi ya lashe zaben.

To har yanzu Amurkawa na nan suna jiran sakamakon zabe a wasu jihohi da ake fafatawa, domin sanin ko Shugaba Mai ci Donald Donald zai ci gaba da jaogarantar kasar, ko kuma abokin hamayyarsa na jam’iyyar Democrat tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden zai maye gurbinsa.

An yi ta gwangwajewa a birnin Washignton DC. Da kuma birnin Miami da ke jihar Florida a daren jiya Talata, yayin da ake dakon sakamakon zaben shugaban kasa tsakanin Shugaba mai ci Donald Trump da kuma abokin hamayyarsa na Democrat Joe Biden.

Har yanzu babu wanda ya samu adadin kuri’a 270 daga cikin kuri’a 538 na wakilai na musamman da ake kira Eelctoral College, wanda ake bukata dan takara ya samu kafin ya lashe zaben.

Shi dai tsarin zaben Amurka, ba yawan kuri’ar da dan takara ya samu a zaben gama-gari ne yake ba shi nasara ba.

Jeremy Myer, Malami ne a Jam’iar George Mason da ke nan Amurka.

Ya ce, “Akwai alamun an yi kan-kan-kan a tsakanin ‘yan takarar biyu ne. Abin mamaki game da wannan zabe, kusan a iya cewa abin da ya faru a zaben 2016 ne yake sake faruwa, lamarin da zai sake komawa kan wadannan jihohi uku na Winsconsin, Michiga da Pennsylvania.”

Asalin jihohin Winsconsin, Michigan da Pennsylvania, jihohi ne na ‘yan Democrat, wadanda Trump ya lashe su a zaben 2016. Duka ‘yan takara biyu sun tafka yakin neman zabe a yankunan cikin kwanakin karshe gabanin a yi zabe.

Cikin sanyin safiyar yau Laraba, daga gidansa na Wilmington da ke jihar Delaware, Biden ya yi kira ga magoya bayansa da su kara hakuri

“Ku ci gaba da yin Imani, za mu yi nasara! Na gode na gode na gode.”

Jim kadan bayan haka, cikin wani sakon Twitter da ya wallafa, Trump ya yi maza maza ya mayar da martani, yana mai cewa "‘yan Democrat na kokarin su sace zaben," sakon da kamfanin Twitter ya ayyana shi a matsayin wanda zai haifar da rudani. Amma daga baya, ya fito yayi magana daga Fadar White House.

“Wannan abu ne mara dadi, a gani na, wannan lokaci ne na alhini. Amma za mu samu nasara, a nawa ganin ma mun riga mun yi nasara.”

Duk da cewa shugaban yana ikirarin samun nasara, za a ci gaba da kidaya kuri’u, kuma ta yiwu abin ya dauki kwanaki kafin a san takamaiman wanda ya samu nasara.

LaTrice Washington, Malama ce a jami’ar Otterbein. Ta ce, “saboda annobar Covid-19, mun ga yadda karin mutane suka yi ta aikawa da kuri’arsu ta gidan waya. Saboda haka, an samu karin mutane da suka bukaci yin zaben ta haka, lamarin da zai sa a dan samu jinkiri wajen (kidayar).”

Biden
Biden

Amurkawa dai sun gudanar da zaben nasu cikin lumana, duk da cewa an girke ‘yan sanda a wasu rumfunan zabe, yayin da jami’an tsaron suka zauna cikin shirin ko-ta-kwana, bayan da aka kwashe lokaci ana zazzafar yakin neman zabe da ya rarraba kawunan jama’a

Trump Biden
Trump Biden

Yayin da aka yi kan-kan-kan a wasu jihohi da dama, aka kuma kai kararraki kotu kan ka’idojin zabe, da watakila za su iya tasiri kan kuri’un da za a kidaya, dole ne yakin neman zaben na Amurka da aka kwashe watanni ana yi ya dauki lokaci kafin a ga karshensa.

Ga rahoton da Mahmud Lalo ya hada muna a cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG