Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ganin Joe Biden Ne Zai Lashe Zaben Shugaban Kasa a Amurka


Dan takarar shugaban kasa a Amurka na jam'iyyar Democrat, Joe Biden a Delaware, ranar 4 ga watan Nuwamban 2020.
Dan takarar shugaban kasa a Amurka na jam'iyyar Democrat, Joe Biden a Delaware, ranar 4 ga watan Nuwamban 2020.

VOA ta yi hasashen tsohon mataimakin shugaban kasa a Amurka, Joe Biden wanda ya dade ana damawa da shi a siyasar Amurka, shi ne ake gani zai lashe zaben shugaban kasar, abin da ke nufin za a rantsar da shi a matsayin shugaban kasa ranar 20 ga watan Janairun 2021.

Hakan zai sa ya zama shugaban Amurka mafi yawan shekaru.

VOA ta yi nazarin bayanan kuri'un da aka kirga a sauran jihohin da suka rage, sannan ta dogara akan sahihancin hasashen da kamfanonin dillancin labarai na Reuters AP suka yi a game da wadanda suka yi nasara a zaben. Ba bu sakamakon zaben daga wata jiha da VOA ta bayar ba tare da Reuters da AP sun bayar da na su hasashen ba.

Biden, dan jam'iyyar Democrat wanda ya shafe shekara 36 a majalisar dattijan kasar, da kuma shekara takwas a matsayin mataimakin shugaban kasa a gwamnatin Barack Obama, ana gani ya shiga gaban shugaban kasar mai ci dan jam'iyyar Republican Donald Trump a zaben shugaban kasar wanda ya yi zafi sosai.

Za a sanar da sakamakon zaben a hukumance, sannan akwai yiwuwar a kalubalanci sakamakon zaben a kotu. Amma dai ana sa rai sakamakon zaben zai tabbata.

Biden ya lashe zaben ne inda ya samu kuri'ar kwaleji fiye da 270 daga cikin 538.

Bayan kafafen yada labarai sun sanar da cewa shi ne ya yi nasara a zaben, Biden ya yi godiya ga Amurkawa bisa ba shi damar jagorancin kasar da suka yi.

Nasarar da ake tunanin Biden zai samu mai yiwuwa ta sa Trump ya zama shugaban Amurka na uku a cikin shekaru arba'in da ya fadi zaben neman wani wa'adi bayan shekara hudu a ofis.

Nasarar ta Biden ta zo ne bayan wasu kwanaki da kammala zaben kasar na ranar Talata, yayin da jami'an zabe a jihohi da dama suka kammala tattara sakamakon miliyioyin kuri'u da aka kada ta hanyar akwatin gidan waya, wadanda mutane suka aika domin gujewa zuwa rumfunan zabe saboda fargabar coronavirus.

Sai dai gangamin yakin neman zaben na Trump ya yi maza ya fitar da wata sanarwa inda ya kalubalanci hangen nasarar ta Biden, sannan ya jajirce cewa zai ci gaba da yakar matakin a kotu har sai an sauya sakamakon.

Jami’ai a jihohi ba sa ayyana wanda ya lashe zabe a hukumance har zuwa tsawon kwana 30 bayan zabe, amma gamayyar manyan kafafe yada labarai sukan yi hangen wanda suke ganin zai lashe zaben idan suka lura cewa babu wasu isassun kuri’u da ba a kidaya ba, wadanda ba za su iya sauya sakamakon ba.

Biden wanda zai kasance mai shekara 78 zuwa lokacin da za a rantsar da shi Idan an har ya yi nasara, zai lashe zaben shugaban kasar ne a yunkurinshi karo na uku, bayan ya kasa yin nasarar ganin jam'iyyar shi ta Democrat ta tsayar da shi takarar shugaban kasa a 1988 da 2008, a lokacin bai samu goyon baya sosai ba.

Mai yiwuwa zai shugabanci gwamnatin Amurka tare da abokiyar takararshi, Sanata Kamala Harris daga California, wacce mai yiwuwa ta zama mace ta farko a shekaru 244 a tarihin siyasar kasar da aka taba zaba a matsayin mataimakiyar shugaban kasa. Mahaifinta dan kasar Jamaica ne sannan mahaifiyarta 'yar India, kuma ita ce mace ta farko wacce ba farar fata ba da ta kasance a tikitin neman mataimakiyar shugaban kasar.

Bayan manufar shugaba Trump ta “America First” wacce a karkashinta, Amurka ta janye daga yarjejeniyoyin kasa da kasa da dama, Biden ya sha alwashin sake mayar da Amurka cikin harkokin duniya da suka hada da yarjejeniyar yaki da sauyin yanayi ta Paris, da kuma yarjejeniyar hana Iran kera makaman nukiliya.

Amurka ta na amfani ne da tsarin dimukradiya wanda ba yawan kuri'u da dan takara ya samu a fadin kasar ne ke sa ya yi nasara a zaben shugaban kasa ba. Jihohin kasar 50 da Washington, D.C. ne suke tabbatar da wanda ya yi nasara ta hanyar lashe kuri'un kwaleji 270 ko fiye daga cikin 538 da ake da su.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG