Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Rage Adadin Masu Neman Mafaka A Kasar


Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump.

Amurka za ta kyale akalla masu neman mafaka, wato 'yan gudun hijira 15,000 ne kawai a shekarar 2021, mafi karanci a cewar wata sanarwa da gwamnatin Trump ta wallafa a rajistar tarayyar kasar a ranar Juma’a.

Amurka za ta kyale akalla masu neman mafaka, wato 'yan gudun hijira 15,000 ne kawai a shekarar 2021, mafi karanci a cewar wata sanarwa da gwamnatin Trump ta wallafa a rajistar tarayyar kasar a ranar Juma’a.

Gwamnatin ta kuma dakatar da shigowar akasarin 'yan gudun hijira daga Syria da Somali da Yemen saboda abinda ta bayyana da barazanar ta’addanci.

Sanarwan ta ce kaiyadewar “ta dace saboda damuwa irin ta al'amuran jin kai".

Wannan adadin wanda yayi kasa daga 18,000 a shekarar da ta wuce kuma kasa sosai da 84,000 na masu neman mafaka da aka karba a shekarar 2016, zai kasance a haka har zuwa watan Janairu har ma fiye idan an samu canji a fadar White House.

Kungiyoyin al'amuran jin kai sun shaida wa VOA cewa adadin ‘yan kasar Syria da Somali da Yemen wadanda aka riga aka ba su mazauni a Amurka ya ninka adadin da aka kayyade.

Ya zuwa 27 ga watan Octoba kungiyoyin sa kai sun tabbatar da a kwai masu neman mafaka mutum 27,023 da ke jira a tantancesu a Amurka.

A cewar kungiyoyin al'amuran jin kai guda biyu, daga cikin adadin, akwai 12,924 daga Somali da 14,084 daga Syria da 15 daga Yemen.

UNHCR
UNHCR

Jennifer Quigley, wata darakta a kungiyar Human Right First, ta ce aikin ba 'yan gudun hira matsugunnai ya na tafiyar hawainiya sannan da wahala. Ta kuma ce wadanda hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya - UNHCR ta bayar da sunansu, suna jira tun sama da shekara daya.

Quigley ta kara da cewa bukatar ta su ta na da matukar wahala sosai, inda kasa da kashi daya cikin dari na masu bukatar mafakar a fadin duniya da kyar suke samun nasarar a wuce musu gaba.

Tace, “matsayin zama dan gudun hijira ya na ba su damar samun kariya a inda su ke. Amma ba zai sa a su matsuguni ba, saboda haka a kwai karuwar su a duniya zuwa miliyan 27 a duniya.”

Matakin da gwamnati ta dauka

Yayin da VOA ta tuntubi ma’aikatar harkokin waje ta Amurka, mai magana da yawun su ya ki bayar da ba’asi a kan ko wadannan ‘yan gudun hijira daga Yamen da Syria da Somalia dake cikin tsarin sama musu matsuguni za’a ki karbarsu bisa bambancin kasa ko kuma karancin kudin da aka samar.

Sanarwar ta ranar Juma’a ta nuna ‘yan gudun hijirar za su iya kasancewa wadannan suka fito daga kasashe da aka sanya wa takunkumi ko wadanda suka gujewa gallazawa ko kuma suke da hujja ta gallazawa saboda bambancin addini.

Ba bu masaniya a game da adadin wadanda za a dagawa kafa dawanda za’a iya ba su damar su wuce daga cikin mutum dubu 27,023

Rashin tabbas na siyasa

Tsawon lokacin da sanarwar za ta dauka ta na aiki ya danganta ne akan wanda ya shiga fadar White House a watan Janairu.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyar Democrat Joe Biden, a lokacin yakin neman zabe ya sha alwashin kara adadin ‘yan gudun hijira zuwa 12,5000.

Manajar sadarwa ta hukumar ‘yan gudun hijira a Amurka, Sara Seniuk ta ce Biden zai iya kara adadin 'yan gudun hijiran a shekara mai zuwa. Yayin da ya ke shirin barin mulki a 2017, Shugaba Barack Obama ya kara adadin 110,000, shi kuma Shugaba Donald Trump ya rage adadin zuwa 45,000.

Ko da a ce za a samu kari a adadin, masana harkar ‘yan gudun hijira sun ce zai dauki locaci kafin a fadada shirin bayan shekaru da aka dauka ana ta ragewa.

A karkashin tsarin na Trump na shekara 2021, a kwai damar karbar mutum 5,000 dake fuskantar tsanantawa na addini da 4,000 na ‘yan gudun hijira daga Iraqi wadanda suka taimaka wa Amurka da 1,000 na ‘yan gudun hijira daga El Salvador da Guatemala da Honduras, ragowar dubu biyar kuma na sauran masu nema.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG