A daren litinin ne shugaban hukumar zaben Nigeria Attahiru Jega ya bayyana sakamon zaben na ranar Asabar inda jam’iyyar dakemulki ta PDP wadda shugaba Goodluck Jonathan yayi takara karakshinta ta sami yawan kuri’un da suka kai miliyan 22,495,187. Ita kuma jam’iyyar hamayya wadda tsohon shugaban Gwamnatin mulkin sojin Nigeria janar Muhammadu Buhari yayi takara karkashinta ta sami yawan kuri’un da suka kai miliyan 12,214,853, ita kuma jam’iyyar CAN da tsohon shugaban hukumar hana cin hanci da Rashawa Nuhu Ribadu yayi takara karkashinta ya sami kuri’u miliyan 2,079,151, sai kuma jam’iyyar ANPP wadda Gwamnan jihar Kano Ibrahim Shekarau yayi takara karkashinta ta sami yawan kuri’un da suka kai dubu 917,012.
A halin da ake ciki, an sami rahotannin tashin rikici a sassan Arewacin Nigeria, rikicin ya biyo bayan rashin amincewar ‘yan hamayya ne da sakamakon zaben da aka bayyana. Ma’aikatan kungiyar agajin kasa da kasa ta Red Cross ta bada rahoton cewa jami’anta sun ga gawarwaki kan titunan kan hanyarsu ta zuwa Asibiti. Anfi yin rikicinn ne a jihohin kano da Kaduna Arewacin Nigeria. An kuma kafa dokar hana yawo ta tsahon sa’o’i 24 a Kaduna inda masu zanga-zanga suka kara da ‘yan sanda a Kaduna da Zaria.
Rahotannin dake fitowa daga Nigeria na cewa an rasa rayuka a dalilin sakamakon zaben Nigeria. ’Yan hamayyar Nigeria sun yi zargin tafka magudi a zaben shugaban kasar na ranar Asabar