Da jin labarin cewa shugaba Goodluck Jonathan ne ya sami nasara, sai tarzoma ta barke a a mafi yawan jihohin Arewacin Nigeria inda Muhammadu Buhari yafi samun kuri’u da goyon baya. Buhari dai Musulmi ne kuma tsohon shugaban Gwamnatin mulkin sojan Nigeria. Rahotannin da ‘yan sandan Nigeruia ke bayarwa na cewa masu zanga-zanga kin amincewa da sakamakon zaben na Nigeria sun bazama kan titunan birnin Kaduna inda aka bada labarin tashin bom a daren Asabar a wani Otel harma mutane takwas suka jikkata. Kazalika ‘yan sanda sun bada rahoton tashin hankali da kone-kone a biranen Kano da Zaria.
Duk da haka jami’an dake nazartar yadda aka gudanar da zaben sun ce anyi zaben cikin ‘yanci da walwala im banda coge-da dan magudin da aka yi jifa-jifa nan da can. A halin da ake ciki, jami’an tsaron Nigeria sun shiga loko-loko a wuraren da aka bada rahoton tashin hankali domin kokarta maido da zaman lafiya a Nigeria. A yadda al’amuran ke tafiya a yanzu haka dai idan har hukumar zaben Nigeria ta ayyana Mr. Goodluck Jonathan shine ya sami nasarar zama sabon shugaban kasa, ba lallai bane aje zagaye na biyu domin fidda gwani ba, domin ya riga ya sami sama da rabin kuri’un da zasu hana sake kaiwa ga zagaye na biyu a zaben.