Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sanar Cewa Jonathan Ne Ya Ci Zaben Shugaban Kasar Nijeriya, Tashin Hankali Ya Barke A Nijeriya


Wasu masu zanga-zanga kenan a Kano.
Wasu masu zanga-zanga kenan a Kano.

Jiya Litini jami’an hukumar zaben Nijeriya sun ce Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan ne ya ci zaben shugaban kasar Nijeriya, a yayin da tashen-tashen hankula ke ta barkewa a arewacin kasar inda Musulmi su ka fi yawa don nuna kin amincewa da sakamakon.

Jami’an na INEC sun ce Mr. Jonathan ya sami sama da kuri’u miliyan 22 (watau 22,495,187) a zaben na ran Asabar, wanda ya kusa ribanya na babban mai kalabalantarsa, tsohon shugaba na mulkin soji Muhammadu Buhari, wanda ya sami sama da miliyan 12 (watau 12,214,853).

Mr. Jonathan ya sami isassun kuri’un da su ka sa ya ketare tsiratsin zabe zagaye na biyu, inda ya sami kashi 57% na kuri’un da aka kada.

Labarin nasarar Jonathan ya sa tashin hankali ya barke a yankin arewacin Nijeriya.

Kungiyar Red Cross a Nijeriya ta kiyasta cewa sama da mutane 270 sun sami raunuka kuma wasu 15,000 sun rasa muhallansu.

Masu goyon bayan ‘yan adawa sun ce an yi aringizon kuri’un ne don haka su ka cinna wa gidaje wuta, su ka kona tayu su ka kuma yi ta jifan ‘yan sanda da duwatsu don nuna bacin ransu game da sakamakon. Babu daya daga cikin jam’iyyun adawan day a rattaba hannu kan sakamakon karshe na zaben kuma jam’iyyar Mr. Buhari ta kalulanci sakamakon a hukumance.

Jiya Litini Shugaba Jonathan ya yi kiran da a kawo karshen tashe-tashen hankula da kuma abin da ya kira fito-na-fito na siyasa. Ya ce babu wanda ya cancanci a zubar da jinin wani dan Nijeriya saboda muradin siyasarsa.

Da yawa a arewacin Nijeriya da Musulmi su ka fi rinjaye sun goyi bayan Buhari, wanda Musulmi ne. Shugaba Jonathan, wanda Kirista ne, ya fi samin kuri’unsa a kudancin kasar inda Kirista su ka fi yawa.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG