Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara, arewa maso yammacin Nigeria tace a saboda tarzomar daya barke a birnn Tsafe, ta dauki matakan gaggawa na maido da zaman lafiya a jihar. Yanzu haka an kafa dokar hana fitan dare daga karfe goma na dare zuwa bakwai na safe. Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar Zamfara, ASP Lawal Abdullahi ya shedawa wakilin sashen Hausa cewa an kama mutane 47 kuma yanzu haka ana yi musu tambayoyi a ofishin yan sandan jihar. Yace idan aka gama bincike duk wanda bashi da laifi za'a sake shi, mai laifi kuma a hukunta shi. A halin da ake ciki kuma jami'an tsaro sun harbe wani dalibi a Tsafe a lokacinda ya fito daga gidansu.
An sakamakon tarzomar daya barke a birnin Tsafe jihar Zamfara, an kafa dokar hana fitan dare.