Magabatan Nijeriya na cigaba da kiraye-kirayen a zauna lafiya a kai zuciya nisa bayan munanan zanga-zangogin da aka yi ta yi a arewacin kasar.
Wani na hannun damar dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar CPC, Janar Muhammadu Buhari (murabus) wanda kuma shi ne dan takarar gwamnan jahar Kaduna a karkashin jam’iyyar CPC AVM Aliyu Ahmed Rufai ya ce sam tashe-tashen hankula ba al’adar jam’iyyarsu ta CPC ba ne.
Day a ke magana da Muryar Amurka, AVM Rufa’I ya ce abin da aka yi bai kyautu ba. “Mu dai mun ce a kasa a tsare don mun san PDP tunda ta ke kan gwamnati a karo na uku ba su taba gudanar da zabe ba tare da magudi ba. Amman ba mu ce a kona gidan kowa bat un kafin zaben. Kuma mu ba mu taba yawo da ‘yan banga ba. Hasalima mun gaya wa jama’a su zamanto masu hakuri.” Inji AVM Rufa’i.
Shi ma wani dattijon arewa, Alhaji Adamu Ciroma yace idan babban al’amari irin zaben shugaban kasa ya faru, abinda ya kamata ya biyo baya shine danne zuciya da hakuri da duk abin da ya faru. Saboda tashin hankali ba a san abinda zai haifar ba.
Adamu Ciroma ya kara da cewa, “Ubangiji Yan a cewa a cikin Alkur’ani Mai Tsarki: Ku ji tsoro ku guji irin fitinar da ke aukuwa saboda ba za ta zabi azzaluman cikinku ta yi das u kawai ba. Idan fitina ta tashi, za ta shafi kowa da kowa ne.
Su ma malaman addinai ba a barsu a baya ba. Shugaban kungiyar Jama’atu Nasril Islam, Alhaji Jaafar Makarfi y ace su a matsayinsu na malaman addinai so su ke jama’a su kwanatar da hankulansu su daina duk tashin tashina, hankali ya koma jikinsu—su natsu.
Ya ce idan aka shiga tashin hankali babu ma yadda za a san ko mene ne ke damun jama’a; me su ke bukata balle ma a yi bincike a yi gyara idan na gyaran ne. Bai kamata a dauki doka a hannu ba. Na yi mamaki ma da aka ce ana kona coci-coci da masallatai. Wannan bai dace ba ko kadan.
A nasa bangaren kuma, shugaban kungiyar Kiristan Nijeriya (CAN), shiyyar jihar Kaduna, Rev Samuel Nyat, ya bayyana abin day a faru da cewa abin bikin ciki ne. Yace Hasalima abinda jama’a ke bukata a yanzu a Nijeriya shi ne shugabannin da za su tabbatar masu da tsaron dukiyoyi da lafiya.
Ya ce ya ji dadin irin jawabin da gwamnan jihar Kaduna ya yi game da rikicin. Don haka ya bukaci dukkan mutanen jihar Kaduna das u cigaba da zama lafiya. “Wannan al’amarin ba addini ba ne. Tsabar siyasa ce kawai,” inji Rev. Nyat.