Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Goodluck Jonathan Ya Doshi Lashe Zaben Shugaban Kasa A Najeriya


Pasta na Goodluck Jonathan a jikin wata babbar mota a Najeriya
Pasta na Goodluck Jonathan a jikin wata babbar mota a Najeriya

Sakamakon da hukumar zaben Najeriya, INEC, ta bayar ya nuna cewa dan takarar na jam'iyyar PDP yayi fintinkau ma sauran 'yan takara

Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan, kusan ya kama hanyar zama kan gaba a sakamakon zaben shugaban kasar Nijeriya, a daidai lokacin da ake c igaba da kidaya kuri’u a wannan kasar da ta fi yawan jama’a a Afirka.

Dandalin Internet na hukumar zaben Nijeriya, INEC, ya nuna cewa Mr. Jonathan na kan gaba da cin jihohi 21 daga cikin jihohi 29 da aka bayyana sakamakonsu. Babban mai kalubalantarsa, Muhammadu Buhari, ya tabuka sosai a bangaren arewacin Nijeriya da ya fito.

Kafin dan takara ya ci ba tare da karawar zagaye na biyu ba, sai ya fi samin yawan kuri’u ya kuma sami akalla rubu’i wato kashi daya cikin hudu na yawan kuri’un da aka kada a jihohi 24 daga cikin jihohi 36 na Nijeriya.

Shugaba Jonathan, wanda Kirista ne daga yankin Naija-Delta mai arzikin man fetur, ya kasance a gaba gaba sosai daga cikin 'yan takarar. Mr. Buhari, wanda tsohon shugaban mulkin soji ne, ya fito ne daga arewacin Nijeriya inda Musulmi su ka fi rinjaye. Ya fadi a zabukan shugaban kasa sau biyu a baya.

An dan sami tashe-tashen hankula masu nasaba da zaben da yammacin ran Asabar, bayan da masu sa ido suka ce zaben ya gudana cikin natsuwa, in banda ‘yan cuwa-cuwa nan da can.

XS
SM
MD
LG