An Rage Jami’an Tsaron Nyako

Admiral Murtala Nyako mai ritaya, gwamnan Jihar Adamawa.

Admiral Murtala Nyako mai ritaya, gwamnan Jihar Adamawa.

​Biyo bayan kazafin da Gwamnan Jihar Adamawa Admiral Murtala Nyako mai ritaya yayi wa shugaban Najeriya Goodluck Jonathan na yunkurin yiwa jama’ar arewacin Najeriya kisan kare dangi, jama’a da dama da kungiyoyi da shuwagabanni na mayar da martani, wasu suna yaba mishi, wasu kuma suna sukarshi.
Rahotanni da yanzu muke samu suce an rage adadin jami’an tsaron dake kula da Murtala Nyako mai ritaya, daga 170 zuwa 30 kacal.

Yanzu dai masana harkar tsaro da kuma wasu kungiyoyin cigaban arewa sun fara mai da martani game da janye wasu jami’an tsaron gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako, da rundunan ‘yan sandan jihar tayi, batun da ke dangantawa da takaddamar da ke akwai a tsakanin fadar shugaban kasar da kuma gwamnan Adamawa, wanda tuni wasu ke mai lakabi da sadaukin arewa.

Shi dai gwamnan Adamawa a ganawarsa da manema labarai a Yola, yace kawo yanzu bai da cikakkiyar masaniya game da janye jami’an tsaron, koda yake yace bai san dalilin yin hakan ba.

“A gaskiya babu wata wasika ko sako da na samu a hukumance, wata kila akwai mataki da suka dauka ne, na inganta tsaro, wanda ba dole bane kowa ya sani,” fassarar kalaman Nyakon wanda yayi da turanci.

A kwanakin baya gwamnan Jihar ta Adamawa, daya daga cikin jihohi uku dake da dokar-ta-baci, Nyako ya dauki alwashin tattara takardun shaidu domin kai karar shugaban Najeriya a kotun bin kadin manyan laifuka ta kasa da kasa, wato ICC a takaice dake can birnin Hague a Netherlands.

Your browser doesn’t support HTML5

An Rage Jami'an Tsaron Nyako - 3'25"