Dr. Bawa Abdullahi Wase, wani masani harkokin tsaro ne a Najeriya “ai abunda Murtala yayi, kamar mutum ne yana bacci kazo ka tashe shi, ya daina yin bacci. Wannan abunda yayi kennan.”
“Gaskiyar lamarin shine duk mai hankali ya riga ya sani, cewa mafi yawan gwamnonin nan, jabu ne. Mafi yawan gwamnonin arewa baragurbi ne. Ba jama’a ne ya dame su ba, abinda ya dame su kazamin dukiyar da wadansunsu suke ta diba suna tarawa”, a cewar Dr. Wase.
“Misali da gwamnonin arewa suna da zuciya, kuma don jama’a suke aiki, ai ko shi shugabansu Babangida Aliyu bai kamata ya zama shugaban gwamnonin arewa ba,” Dr. Wase yayi karin bayani.
Wannan batu ne wanda ba’a tsammanin zai tsaya a haka, saboda a kwanakin baya gwamnan jihar ta Adamawa, daya daga cikin jihohi uku dake da dokar-ta-baci, Nyako ya dauki alwashin tattara takardun shaidu domin kai karar shugaban Najeriya a kotun bin kadin manyan laifuka ta kasa da kasa, wato ICC a takaice dake can birnin Hague a Netherlands.
A halin yanzu dai gwamnatin tarayya ta rage yawan jami’an tsaro dake gadin gwamnan Jihar Adamawan daga 120 zuwa 30 kacal, wanda kawo yanzu babu cikakken bayani daga hukumomin abinda ya shafa, yayin da jiragen sama masu saukar ungulu na soji ke cigaba da shawagi.