Taron ya mayarda hankali ne kan yadda za'a magance maganar tsaro a arewa da kuma yadda za'a habbaka tattalin arzikin yankin.
Amma yayin da jami'an tsaron Najeriya ke buga kirjin suna samun nasara kan 'yan Boko Haram wasu gwamnonin basu gamsu da yadda jami'an tsaro ke aikinsu ba ko kuma yadda da ikirarinsu. Gwamnonin dake jihohin da aka kafawa dokar ta baci basu yadda da matakan da ake dauka ba.
Gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako yace su har yanzu basu gamsu da matakan da ake dauka ba. Yace 'yan Boko Haram zasu kwashi motoci wajen talatin da bakwai idan zasu je su kone wani wuri kuma jami'an tsaro su ce basu gansu ba domin daga iyakar wata kasa suka fito. Yau shekara da shekaru ana kashe mutane da rana tsaka da safe ko da daddare. Babu abun da ake yiwa 'yan ta'adan. Yace kuma har yanzu gwamnati bata iya ta gano su wanene ke bayan 'yan Boko Haram ba. Yace sun shigo da kayan yaki da bama bamai daga ina suka samo su? Ta yaya ma suka iya suka shigo dasu kasar.
Amma jama'ar dake zama tsakanin iyakar Adamawa da Borno sunce hankulansu sun fara kwatanwa domin komi ya daidaita. Kura ta lafa. Jama'a suna cigaba da harkokinsu na yau da kullum. Jami'an tsaro sun shgo suna kuma kama mutanen da basu yadda dasu ba.
Ga karin bayani