Kiran wadanan kungiyoyi na zuwa ne a yayin da kotun CEDEAO a zamanta na hantsin wannan juma’a ta umurci hukumomin CNSP su mayar da shugaba Mohamed Bazoum kan mukaminsa.
Mataimakin shugaban gamayyar kungiyoyin farar hula ta DCTR Tsayabou Lawal Salao ya jaddada bukatar amfani da hanyoyin sulhu wajen kunce kullin da ya sarke bayan juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023.
Canjin matsayin da aka samu daga bangaren CEDEAO a karshen makon jiya idan aka kwatanta da yadda ta ke kallon lamarin da ya faru a Nijar bayan hambarar da shugaba Bazoum babban ci gaba ne injisu saboda haka suka bukaci hukumomin mulkin sojan CNSP su yi na’am da bukatun da ECOWAS ta zo da su.
Shugaban kungiyar Voix des sans Voix Nassirou Saidou kusa ne a DCTR. Ya kuma ce tunda kungiyar da farko ba ta yarda cewa an yi juyin mulki ba amma kuma yanzu ta amince kuma ta yarda sojojin juyin mulki su tattauna da shugabanin kasashen, kamata yayi sojojin suma su matso a samu a warare takunkumin da ke gallaza wa talakawa
Sai dai a dai bangare a washegarin taron na 10 ga watan disamba wasu kungiyoyin na daban sun yi kiran majalissar CNSP ta dauki matakin janye Nijar daga CEDEAO saboda zargin saba wa tsarin ayyukanta, shawarar da gamayyar DCTR ke ganin ta a matsayin ingiza mai kantu ruwa.
A wani abinda ke da alaka da wannan kiki kaka kotun ECOWAS a zamanta na wannan juma’a ta sanar da samun hukumomin mulkin sojan Nijer da tauye ‘yancin hambararren shugaban kasa Mohamed Bazoum saboda haka ta umurce su su gaggauta sakinsa daga inda yake tsare su kuma mayar da shi kan kujerarsa.
A yayinda a siyasance tuni shirin sasanta bangarori ya kankama domin ko a yammacin jiya alhamis shugaba FAURE na Togo ya turo da Ministan harkokin wajensa Robert Dussey zuwa birnin Yamai inda suka gana da Fira Minista Lamine Zeine, Ministan na Togo ya kuma sanar cewa, sun fara magana kan yadda za a tsara al’amuran gwamnatin rikon kwarya.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5