Amurkawa 11 Ne Suka Mutu A Harin Da Hamas Ta Kai Isra’ila - Biden

Biden a lokacin da yake bayani akan yakin Isra’ila da Hamas

Isra'ila ta kara zafafa hare-haren sama da take kai wa a zirin Gaza tare da killace shi daga samun abinci, man fetur, da sauran kayayyakin more rayuwa.

WASHINGTON, D. C. - Wannan mataki da Isra’ilan ta dauka ramuwar gayya ne kan kutsen da mayakan Hamas suka yi wanda ya yi sakamakon mutuwar daruruwan Yahudawa.

Israel/Palestinians

Hamas a nata bangaren, ta yi barazanar halaka Yahudawan da suka kama idan har aka kai hari kan fararen hula ba tare da gargadi ba.

Mayakan Hamas da suka kai harin na Asabar a kudancin Isra’ila, sun yi ikirarin kama Yahudwa sama da 100 ciki har manyan jami’an tsaron kasar.

Wani mutum ana tisa keyarsa

A yini na uku da aka kwashe ana yakin, Isra'ila na ci gaba da samun gawarwaki daga harin da Hamas ta kai a karshen mako a garuruwan kudancin Isra'ila.

Akalla Amurkawa 11 ne aka tabbatar da mutuwarsu a harin na ba-zata da kungiyar Hamas din ta kai, kamar yadda shugaban Amurka Joe Biden ya fada.

Israel/Palestinians

Biden ya kuma “kyautata zaton” akwai Amurkawa cikin wadanda mayakan Hamas ke garkuwa da su a halin yanzu, yayin da wasu 'yan Amurkan ba a san inda suke ba bayan harin da aka kai.

"Ina mai nuna juyayina ga dukkan iyalan da wannan mummunan al'amura suka shafa cikin 'yan kwanakin nan.

"Alhinin da wadannan iyalai suke fuskanta saboda rashin da suka yi, abu ne da ba zai misaltu ba.” In ji Biden.

Shugaba Biden da Sakataren harkokin wajen Amurka Antoni Blinken a lokacin tattaunawa akan yakin Isra’ila da Hamas

Ya jaddada cewa ma'aikatar harkokin wajen Amurka tana ba da taimako ga 'yan kasar Amurka da ke Isra'ila a halin yanzu, yana mai cewa akwai tayin zabin barın Isra’ila ta jiragen sama ko ta kasa, ga wadanda suke bukatar barin kasar.

Biden ya kuma ce jami'an tsaron Amurka na "sa ido sosai" kan yiwuwar barazanar cikin gida da ka iya tasowa daga hare-haren na karshen mako.

Al-Agsa

Hamas ta kaddamar da hare-haren nata na ranar Asabar ne bisa ikirarin yadda Isra’ila take mamaye yankin Masallacin Kudus da kuma yadda yankin Gaza ke rayuwa karkashin danniyar mulkin Isra’ila, zargin da Isra'ilan ke musantawa.

-AP