Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da mayakan Hamas da dama suka kutsa cikin Isra'ila ta kan iyakar da ke da tsauraran matakan tsaro a wurare da dama, tare da yi wa kasar ta Isra’ila dirar mikiya.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce akalla Isra’ilawa 200 sun mutu, yayin da wasu sama da 1,100 kuma suka jikkata sakamakon arangamomin bindiga daban-daban a wurare sama da 20 a cikin Isra’ila.
Asibitoci a Isra'ila suna kula da daruruwan mutanen da suka jikkata, ciki har da wasu da dama da ke cikin mawuyacin hali.
Firayim Minista Benjamin Netanyahu ya ayyana cewa Isra'ila "tana cikin yaki" kuma ya yi kira da a tattara tarin sojoji.
Netanyahu ya ce Isra'ila za ta maida kakkausan martani kan Hamas, wanda kuma nan take ta kaddamar da harba makamai zuwa Gaza.
A Gaza din jami’an kiwon lafiya sun ce an kashe sama da mutane 230, yayin da kuma aka raunata wasu 1,600.
Hamas ta ce ta harba roka 150 zuwa cikin Tel Aviv da yammacin ranar Assabar, domin martani kan harin da Isra’ila ta kai ta sama da ya ruguza wani ginin bene mai gidaje sama da 100.
Mataimakin Shugaban Hamas Saleh al-Arouri ya fadawa gidan talabijin na Al Jazeera cewa, kungiyar tana tsare da adadi mai yawa na Isra’ilawa da ta kama, ciki har da manyan jami’ai.
Ya ce Hamas tana da isassun mutanen da take tsare da su, da za su sa Isra’ila ta saki dukan Falasdinawan da take tsare da su a gidajen yari.
Rundunar sojin Isra’ila ta tabbatar da cewa ana tsare da ‘yan Isra’ila a Gaza. Kakakin rundunar sojin Isra’ila ya ce kasar na kokarin tattara hancin dubban sojan ko-ta-kwana, haka kuma tana shirin shiga yaki a fagen daga ta arewa, kan mayakan Hezbollah na Lebanon.
Dandalin Mu Tattauna