Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firai Ministan Isra’ila Ya Janye Korar Da Ya Yi wa Ministan Tsaro


Firai Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu
Firai Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu

Firai ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya fada a ranar Litinin zai bar Ministan Tsaro Yoav Gallant a mukaminsa bisa la’akari da yadda matsalar tsaro ke kara ta’azzara, yana mai sauya matakin korar ministan da ta janyo zanga -zanga tare da tayar da hankula a kasashen waje.

A cewar Netanyahu, su biyun sun warware rashin jituwar da ke tsakaninsu kan kiran da Gallant ya fito fili ya yi a watan da ya wuce na dakatar da shirin gwamnati na yin garambawul ga sashen shari’a, wanda Gallant ya ce ya zama barazana ga tsaron Isra’ila.

A makon da ya wuce ne dai Netanyahu ya sanar da cewa zai jinkirta sallamar ministan.

“Na yanke shawarar ajiye banbance-banbance da ke tsakaninmu,” Netanyahu ya fada wa taron manema labarai a ranar Litinin. Ya ce su biyun sun yi aiki kafada da kafada a cikin makonnin biyu da suka wuce.

An kashe wani dan yawon bude dan kasar Italiya yayin da wasu mutane biyar suka jikkata a wani hari da aka kai da wata mota a birnin Tel Aviv a ranar Juma’ar da ta wuce sa’o’i bayan da aka kashe wasu mata ‘yan uwa biyu ‘yan Isra’ila da mahaifiyarsu a wani harin harbi da aka kai a Yammacin gabar Kogin Jordan.

Hare-haren, bayan da aka shafe tsawon dare ana kai hare-hare a kan iyakokin Gaza da Lebanon, ya kara dagula zaman dar-dar tsakanin Isra’ila da Falasdinu, biyo bayan farmakin da ‘yan sandan Isra’ila suka kai a Masallacin Al-Aqsa a birnin Kudus a cikin makonnan.

Rikicin dai ya yi barazana karuwa ne a lokacin da Isra’ila ta mayar da martani game da harba makaman roka ta hanyar kai hari kan wuraren da ke da alaka da kungiyar Hamas a Gaza da kudancin Lebanon, amma fadan ya lafa a ranar Juma’a.

Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da aka gudanar a ranar Lahadi da ta wuce, daga gidan talabijin na Channel 13 News na Isra’ila, ya nuna cewa jam’iyyar Lukud ta Netanyahu za ta yi asarar sama da kashi daya bisa uku na kujerunta idan har aka gudanar da zabe a yanzu, kuma Netanyahu ba zai samu rinjaye tare da abokannan kawancensa masu ra’ayin rikau.

Netanyahu ya shaida wa manema labarai cewa “Ban damu da kuri’ar jin ra’ayin jama’ar ba.”

Reuters

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG