Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Ghana Ta Yi Allah Wadai Da Harin Hamas Akan Isra’ila


Shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo

Gwamnatin Ghana ta kuma yi kira ga kungiyar Hamas da ta janye mayakanta daga kudancin kasar ta Isira'ila ba tare da bata lokaci ba.

KUMASI, GHANA - Kiran na gwamnatin Ghana na zuwa ne biyo bayan farmakin da kungiyar Hamas ta kaddamar a kudancin Israila, abin da ya yi ajalin daruruwan mutane tare da jikkata wasu da dama. Sai dai kasar ta kuma bukaci da a yi zama a teburin sulhu tsakanin kasashen biyu domin ganin an samu mafita maimakon gwabza fada da zai iya janyo asarar rayuka tare da barnata dukiya.

Kusan mutane 1,000 aka kashe a yakin Israel da Hamas
Kusan mutane 1,000 aka kashe a yakin Israel da Hamas

Acikin wata sanarwar da ofishin Ministan harkokin wajen Ghana ta fitar ta ce Gwamnatin Ghana na Allah wadai da wannan hari da Hamas ta kai wa Israila tare da kira ga Hamas ta janye dakarunta daga kudancin Isira'ila ba tare da bata lokaci ba.

Sanarwar ta kuma kara da cewa yayinda Ghana ke ci gaba da ayyana goyun bayanta ga duk wani matakin da Israila zata dauka domin kare kanta, tana kira ga Isira'ila da ta yi taka tsantsan wajen maida martani akan Hamas. Sanarwar ta kuma bukaci da bangarorin biyu da su yi zama a teburin sulhu domin samar da maslaha.

Israel - Palestinians
Israel - Palestinians

To sai dai tuni Firai Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce Isra'ila za ta maida martani mai zafi kan mayakan Hamas da suka kai wa kasarsa hari ranar Asabar da ta gabata.

Masu sharhi na ganin wannan sabon fada da ya barke tsakanin kungiyar Hamas da Isira'ila zai iya jinkirta wani yunkurin karfafa alaka tsakanin Isira'ila da wasu kasashen Larabawa, musamman Saudiyya da ake kallon huldarsu za ta iya taka muhimmiyar rawa akokarin shawo kan rikicin Isira'ila da Falastinu inji Irbad Ibrahim mai sharhi kan harkar tsaro da diflomasiyya.

Hayaki na tashi a sama a bangaren Israeli bayan da mayakan Hamas suka afka kudancin Israel - Daga Gaza, Oct. 7, 2023.
Hayaki na tashi a sama a bangaren Israeli bayan da mayakan Hamas suka afka kudancin Israel - Daga Gaza, Oct. 7, 2023.

Irbad Ibrahim ya kuma kara da cewa kamata ya yi da kasashen su yi kokarin kauce wa kaima raunannu farmaki yayin musayar luguden wuta tsakaninsu. Ya ce "abin da za mu yi kira shi ne a kiyaye hakkoki da rayuka na mata masu juna biyu, mata masu zaman kansu da yara da tsofaffi dama matasan da ba su cikin wannan fada. Sannan kuma ya kamata Majalisar Dinkin Duniya ta taka rawar gani domin ganin an tsagaita wuta nan bada jimawa ba ko kuma ayi asarar rayuka masu yawa"

Israel Palestinians
Israel Palestinians

Alkaluman baya bayan nan sun nuna an kashe Israilawa akalla 600, ciki har da sojoji 44, sannan fiye da 1,500 suka jikkata. Jami'ai a Gaza sun ce mutane 313 ne suka mutu a yankin, yayin da wasu kusan 2,000 suka jikkata. Wani jami'in Isira'ila ya ce sojojin kasar sun kashe mayaka 400 tare da kama wasu da dama.

Saurari cikakken rahoto daga Hamza Adam:

Gwamnatin Ghana Ta Yi Allah Wafai Da Harin Hamas Akan Isra’ila.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG