WASHINGTON, D. C. - Yayin da jami'an Amurka suka bukaci Isra'ila da ta taimaka wajen fito da wani tsari dalla dalla kan yadda za a gudanar da mulki a Gaza bayan yaki, zuwa yanzu kalaman na Campbell su ne mafiya fitowa karara zuwa yanzu da wani babban jami'in Amurka ya yi na nuna cewa dabarun soji da Isra'ila ta ke amfani da su a halin yanzu ba za su haifar da sakamakon da take bukata ba.
"Ta wani bangaren, muna neman sanin ka'idar nasarar," in ji Campbell a taron matasa na NATO a Miami. "Wani lokaci idan muka saurari shugabannin Isra'ila sosai, su kan yi magana ne yawanci kan batun yin gagarumar nasara a fagen fama, cikakkiyar nasara," in ji shi.
"Ba na tsammanin mun yi imanin cewa hakan yana iya yiwuwa ko zai yiwu kuma wai wannan al’amari ya yi kama da yanayin da muka tsinci kanmu a ciki bayan tashin hankalin 9/11, inda bayan an kawar da farar hula sai kuma aka ci gaba da yawan tashin hankali da tawaye."
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu dai ya sha alwashin yin "cikakkiyar nasara" kan Hamas, kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa da ta kai wa Isra'ila hari a ranar 7 ga watan Oktoba tare da kashe mutane 1,200 da kuma yin garkuwa da wasu 250.
A martanin da ta mayar, Isra'ila ta kai hare-hare ba kakkautawa a zirin na Gaza, inda ta kashe mutane sama da 35,000 bisa ga alkaluman ma'aikatar lafiya ta Gaza, baya ga maida cinkusasshen karamin yankin zuwa kufai.
-Reuters