Kwanaki bayan da dakarun Isra’ila suka yi luguden hare-haren saman da suka yi sanadiyyar kisan ma’aikatan jin-kai su 7, fadar White House ta ce Biden ya jaddadawa shugaban na Isra’ila ta wayar tarho cewa “ba mu goyon bayan harin da aka kai wa ma’aikatan jinkai ba, sannan ba za mu amince a ci gaba da irin yanayin jin-kan da ake ciki ba.
Ya nuna cewa Biden ya kuma bukaci daukan sabbin matakai don kare fararen hula da kuma bukatar dakatar da bude wuta ba tare da bata lokaci ba a rikicin da aka kwashe akalla watanni 6 ana gwabzawa.
Amurka, babbar kawar Isra'ila, ta yi tsayin daka da goyon bayan yakin kasar yahudawa da kungiyar Hamas, wanda ya faro bayan harin da Hamas ta kai Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 1,200 tare da kama mutane kusan 250 da aka yi garkuwa da su.
Martanin da Isra'ila ta kai ya kashe Falasdinawa fiye da 33,000 a Gaza, yawancinsu mata da yara, a cewar jami'an kiwon lafiyar Falasdinu.
Dandalin Mu Tattauna