Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Ta Sha Alwashin Ci Gaba Da Kai Hari Rafah, Bayan Hamas Ta Ce Ta Amince Da Tsagaita Wuta


ISRAEL-PALESTINIANS/GAZA
ISRAEL-PALESTINIANS/GAZA

Kungiyar mayaka ta Falasdinu a jiya Litinin ta amince da shawarar tsagaita bude wuta a Gaza daga masu shiga tsakani, sai dai Isra'ila ta ce sharuddan ba su biya bukatunta ba, kuma za ta ci gaba da kai hare-hare a Rafah yayin da take shirin ci gaba da tattaunawa kan yarjejeniyar.

WASHINGTON, D. C. - Abubuwan da ke faruwa a yakin da aka kwashe watanni bakwai ana yi sun zo ne a daidai lokacin da sojojin Isra'ila suka kai hari a Rafah da ke kudancin Gaza daga sama da kasa tare da ba da umarni ga mazauna wasu sassan birnin da su tashi daga wuraren, wadanda su ka kasance mafaka ga Falasdinawa sama da miliyan guda da suka rasa matsugunansu.

Kungiyar Hamas ta bayyana a takaice cewa shugabanta Ismail Haniyeh ya sanar da masu shiga tsakani na Qatar da Masar cewa kungiyar ta amince da kudirinsu na tsagaita bude wuta.

Ofishin Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce daga baya, shawarar tsagaita wutar ta gaza kan bukatun Isra'ila amma Isra'ila za ta tura tawagar da za ta gana da masu shiga tsakani don kokarin cimma matsaya

Ma'aikatar harkokin wajen Qatar ta ce tawagarta za ta nufi birnin Alkahira a ranar Talata don ci gaba da tattaunawa kai tsaye tsakanin Isra'ila da Hamas.

A cikin wata sanarwa da ofishin Netanyahu ya fitar, ya kara da cewa majalisar ministocinsa na yaki ta amince da ci gaba da kai farmaki a Rafah. Ministan harkokin wajen kasar Jordan Ayman Safadi ya fada a shafin sada zumunta na X cewa Netanyahu na yin barazana ga yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta hanyar kai harin bam a Rafah.

Wani jami’in Isra’ila da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce shawarar da Hamas ta amince da shi, wani tsari ne mai cike da rashin albarka na tayin Masar din, kuma ya kunshi abubuwan da Isra’ila ba za ta amince da su ba.

“Wannan ya yi kama da wata dabara da aka tsara ta sawa aga kamar Isira’ila ce ba ta son a cimma ma yarejejeniyar,” in ji jami'in na Isra'ila.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka Matthew Miller ya ce Amurka za ta tattauna martanin Hamas da kawayenta a cikin sa'o'i masu zuwa, kuma yarjejeniyar "za a iya samun biyan bukata".

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG