Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Ta Halaka Falasdinawa 22 A Harin Da Ta Kai Kudancin Birnin Rafah


Gaza
Gaza

Hare-haren da Isra'ila ta kai a kudancin Gaza cikin dare ya yi sanadiyar mutuwar mutum 22 ciki har da yara kanana 18, jami'an kiwon lafiya suka ce a fada a ranar Lahadi, a daidai lokacin da Amurka ke kokarin neman amincewa da karin biliyoyin daloli na taimakon sojojin Isra'ila, kawarta.

WASHINGTON, D. C. - Isra'ila ta kai hare-hare ta sama kusan kowacce rana a Rafah, inda fiye da rabin al'ummar Gaza miliyan 2.3 suka nemi mafaka daga fada a wasu wurare.

Ta kuma sha alwashin fadada hare-haren da take kai wa kungiyar ta Hamas ta kasa har zuwa birnin da ke kan iyaka da Masar duk da kiraye-kirayen da ake yi na tsagaita wuta ciki har da Amurka.

“A cikin kwanaki masu zuwa, za mu kara matsin lamba ta hanyar siyasa da na soji a kan Hamas domin ta haka ne kadai za mu dawo da mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma samun nasara. Za mu kara kai wa Hamas munanan hari nan ba da jimawa ba," in ji Firaiminista Benjamin Netanyahu a cikin wata sanarwa. Amma bai bayar da cikakken bayani ba.

Harin farko da Isra'ila ta kai a Rafah ya kashe wani mutum, matarsa da kuma yaronsu mai shekaru 3, a cewar asibitin Kuwaiti da ke kusa, wanda ya karbi gawarwakin. Matar tana dauke da juna biyu kuma likitocin sun ceci jaririn, in ji asibitin. Harin na biyu ya kashe yara 17 da mata biyu daga danginsu.

Yakin Isra'ila da Hamas dai ya kashe Falasdinawa sama da 34,000, a cewar jami'an kiwon lafiya na yankin, akalla kashi biyu bisa uku na yara da mata.

Isra’ila ta fara kai hari yankin na Gaza ne bayan harin da mayakan Hamas suka kai cikin yankinta wanda ya halaka mutum 1,200 a ranar 7 ga watan Oktoban bara.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG