WASHINGTON, DC —
A shirinmu na Nishadi a yau mun sami zantawa da wani mai bada umarni amma fa na fina-finai da wakokin Olademiji Victor Sunday wanda aka fi sani da DMej yace ya shafe shekaru 8 yana wannan sana’a.
Koda yake Victor Sunday fannin akanta ya karanta amma yace sha’wace ta ja shi ga wannan harka , inda ya koyi aikin da kansa tare da taimakon yanar gizo wato {Internet}.
A shekaru 8 da yayi a wannan harkar ya yi aikin wasu fina-finai amma wadanda ake sa wa a gidajen talabijin sai wasu yan kalilan da jama'a ke sawa a bidiyo a gidajensu .