Tsohon shugaban kasar Amurka Harry Truman, ya zama tsohon shugaban kasar Amurka na 4, da yafi karfi a cikin jerin tsofaffin shugabanin Amurka. A iya tsawon shekaru 7 da wata 8, da yayi yana mulkin kasar ya gabatar da dokoki 907, kuma ya nada alkalan alkalai na kotun koli guda 4, kuma ya saka hannu a wasu dokokin kasa-da-kasa guda 16, da babu shugaba da ya taba yin haka.
Tsohon shugaba Theodore Roosevelt, shine na 5, ya zama shugaba da yafi kowane shugaba zama cikin aiki a tsawon shekaru 7 da wata 5 da yayi yana shugabanci. Shine kuma shugaba da yafi kanana shekaru, ya kuma saka hannu a kan dokoki da suka kai 1,081, haka ya zama mutun na farko da ya fara yaki da cinhanci da rashawa a tsakanin ‘yan kasuwa.
Shi kuwa tsohon shugaba Dwight D. Eisenhower, shine shugaba na 6, a cikin jerin tsofaffin shugabannin kasa masu karfi, ya sa hannu a kan dokoki 484 a lokacin mulkin shi, shugaban dai yayi amfani da karfin shi wajen gabatarwa, ya kuma kwashe zamani 2 a ofis, duk a lokacin ya rantsar da alkalan alkalai 2 na kotun koli. Irin tsarin shugabancin shi yasa ya zama shugaba da kowa zai yi sha’awa.