Babban kamfanin nan na Google ya hada hannu da hukumar UNICEF da tallafawa kungiyoyin da kudi dalar Amurka miliyan guda domin kokarin gudanar da ayyukan gano wurare daban daban da annobar cutar Zika ke ci gaba da bazuwa a duniya.
Kungiyar injiniyoyi kwararru a bangaren zana taswira da kimiyya masu ayyukan sa kai na kamfanin Google ne ke taimakawa hukumar UNICEF wajan kera wata manhajar na'ura mai kwakwalwa wadda zata rika samo bayanai daga yanayi da kuma yadda jama'a ke shiga da fita daga wan wuri zuwa wani domin gano barkewar annoba cututtuka.
Babban makasudin wannan bincike shine domin a gano hatsarin cigaba da yaduwar cutar Zika a yankuna daban daban na duniya domin taimakawa hukumar UNICEF da kungiyoyi masu zaman kansu sanin wuraren da yakamata su mayar da hankali da amfani da lokacin su da kuma kayan aiki.
Za'a karkata tallafin kudin dalar Amurka miliyan guda ne wajan rage yawan adadin sauron dake yada wannan cuta a fadin duniya, da kuma inganta magunguna da samar da rigakafin cutar.
Cutar mai saurin yaduwa kuma mai sa a haifi jarirai da karamin kokon kai da motsewar kwakwalwa ta yi illa a sama da kasashen yankin Latin Amurka ashirin.