A wani bincike da wasu masana kimiyar hallitu ke gudanarwa a wani kogo da ke kasar Slovania. Suna kokarin gano wata halitta da ta bace tun kimanin shekaru milliyan 15. Ita dai wannan halittar ta wata dabba da ake kira “Dragon” a turance, ana danganta wannan dabbar da aman wuta, wasu masana tarihi na ganin cewar wannan dabbar batayi rayuwa a duniya mutane ba.
Masu binciken sun bayyanar da wasu kwai masu yawa da suka kai guda 57 da suka samo a cikin wani kogo, acewar su, sun ga wasu halittu masu kama da dabbar dragon da ke fitar da wuta daga bakin su a cikin kogon. Yanzu dai haka an samar da kyamarori da suke akan wadannan kwayayen na tsawon awowi 24, don ganin yadda zasu kyankyashe kwan.
Suna tsanmanin wadannan dabbobin sun rayu sama da shekaru 100, a cikin kogon, kuma suna iya rayuwa har na tsawon shekaru 10 batare da sunci abinci ba. A shekarar 2013 suka fara ganin irin wadannan kwain, amma daga bisani dabbobin sun shanye kwan, amma a wannan karon sun samu damar kwashe sama da kwai 50, wanda suke sa ran kyankyashe su nan bada dadewa ba, kuma ana sa ran mutane zasu halarci kallon kyankasar kwan.Daga nan dai zasu bayyanar da sakamakon binciken su.