A karon farko tun bayan barkewar yaki a kasar Syria, an sami daukewar wutar lantarki a duk fadin kasar a sanyin safiyar jiya Alhamis, sannan kamfanin dillancin labaran kasar wato SANA yace, har yanzu ba a san dalilin daukewar wutar ba, amma ma’aikata na ta kokarin shawo kan matsalar daga yanki zuwa yanki.
Kwararru daga gwamnatin sun bayyana cewa hasken wutar zai samu nan da sa’o’i 12 masu zuwa a duk fadin kasar.
Wata ma’aikacin hukumar Lantarkin kasar ta fadawa Muryar Amurka ta wayar tarho cewa, wannan matsala ce ta na’urori da kan faru a sauran kasashen duniya.
Sai dai jami’ar ta ki yarda ta bada wani karin bayani bayan wannan.
Wata majiyar daga Ma’aikatar wutar ta bayyanawa kamfanin dillancin labaran na SANA cewa, kwararru sun shawo kan matsalar a mafiya yawan garuruwan kasar da yaki ya daidaita.
Wani mai tsokaci yace, a baya Syria ba ta yarda ta bada bayanin matsalolin da ke faruwa a ma’aikatun kasar.