Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa Ga Maganin Tsoron Kyakyawar Budurwa Da Gabatar Da Kai


Wani abu da kan karya lagon matasa a dai-dai lokacin kuruciyar su, wanda hakan kan iya zama wani koma baya a iya tsawon rayuwar su. Akwai bukatar matasa su iya magance wannan makarin tun kamun su kai wani mataki a rayuwa. Wasu masana sun gano wani magani da ba'a bukatar sai an sha.

Sau nawa kuke jin cewar kuna tsoron jarabawa, ko kuma shakkar tattaunawar gwaji na daukar aiki “Interview” ko tunkarar wata budurwa da ta burge ku? Akwai yadda zakuyi ku magance wannan matsalar tun kamin tafi karfin ku a rayuwa. A dai-dai loacin da mutun yaji cewar yana tsoron magana ko aiwatar da wani abu, akwai bukatar mutun ya dauki lokaci ya nunfasa, yayi nunfashi kamar sau 12 zuwa 16 cikin minti 1. Hakan zai bama kwakwalwar mutun damar tunani da aiki yadda ya kamata cikin natsuwa.

A wannan lokacin zuciya itama ta samu karfin da take bukata da bazai sa mata wani tsoro ba, a wannan dan tsakanin mutun zai iya aiwatar da abubuwa da dama idan yana cikin lokacin natsuwa. Duk wanda ya gwada aiwatar da wadannan matakan bi-da-bi zai ga sakamako da zai kara karfafa mishi zuciya da ba zai ji shakkar fadan gaskiya ba, koda kuwa wajen bayyanar da manufar shi ne a karon farko da ya tunkari wata kyakyawar budurwa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG