Babban koc mai rukon kwarya na kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Samson Siasia ya gayyaci ‘yan wasa 42 da zasu kara da Egypt a wasan shiga cin kofin nahiyar Afirka na shekarar 2017.
Najeriya zata marabci kasar Egypt a jahar Kaduna ranar 25 ga watan Maris, haka kuma bayan kwanaki hudu itama Egypt din zata marabci Najeriyar.
Cikin ‘yan wasan da aka gayyata sun hada da ‘yan wasa ashirin dake zama a kasashen waje da kuma ‘yan wasa ashirin da biyu dake gida.
A cikin tsofaffin hannu da aka gayyata sun hada da John Obi Mikel tare da Odion Ighalo mai bugawa kungiyar Watford wasa, da Ahmed Musa na CSKA Moscow Eldeson Echiejile na Monaco tare da Lazio’s Ogenyi Onazi.
A cikin kananan fitattun zaratan ‘yan wasan kuma sun hada da Kelechi Iheanacho na kungiyar Manchester City, da Alex Iwobi mai bugawa Asernal na cikin ‘yan wasan, a yayin da kuma Victor Moses na kungiyra West Ham, da Aaron Samuel na kungiyar Lokomotive Moscow, da mai tsaron gidan dake zama a kasar Afirka ta Kudu Akpeyi zasu dawo gida.