Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ziyarar Samantha Power Kamaru Tayi Sanadiyar Mutuwar Wani Matashi


Samantha Power Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya
Samantha Power Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Samantha Power ta kai ziyara a jihar Arewa Mai Nisa, domin ganin irin ta’adin da maharan Boko Haram sukayi, har ma da ziyarar yan Gudun Hijirar Nijeriya sama da Dubu 50 wadanda suke jibge a kauyan Minawawo. Sai dai cikin tawagar ta wata mota ta buge wani matashi dan kasa da shekaru 15 nan take ya mutu.

A yayin da tawagar motocin jakadiyar ke wucewa ta wani kauye sai matashin yayi yunkurin tsallaka hanya, daya daga cikin motocin da ke wannan tawaga ta kade shi kuma nan take ya Allah ya dauki ransa.

Sai dai Musa Usaini, wanda yake mai rajin kare yancin bil Adama a Kamaru, yayi kira ga Majalisar Dinkin Duniya, da ta fara da taimakawa yara da wadanda aka kashe da kayayyakin da suke bukata kafin a yi maganin Boko Haram din. Har ma yace dole sai an biya iyayen wannan yaro diyyar dansu.

Shima Alhaji Sani Canga, mai sanya idanu kan sha’anin gudanar da mulkin kasar jamhuriyar Kamaru, yayi kira ne da gwamnati da ta mayar da hankali wajen duba faruwar irin wannan hatsari ta kuma dauki matakin da ya dace.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG