Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: Najeriya ta Kawo Sojojin Kasashen Waje su Yaki Boko Haram


Ranar Asabar 7 ga watan Maris, 2015 a garin Mao dake kasar Chadi, dakarun Najeriya na musamman suka yi atisahin kwaikwayon yadda zasu kwato wadanda ake garkuwa dasu.
Ranar Asabar 7 ga watan Maris, 2015 a garin Mao dake kasar Chadi, dakarun Najeriya na musamman suka yi atisahin kwaikwayon yadda zasu kwato wadanda ake garkuwa dasu.

Sojojin kasashen waje dake yaki a Najeriya sun kara tsaurara matakan tsaro yayin da zaben shugaban kasake kunnowa inda ‘yan takarar dake kan gaba suke kunnen doki.

A ranar alhamis din nan wasu Sojin Najeriya suka fada ma sashin Hausa na muryar Amurka cewar Sojin Afirka ta kudu da sauran sojojin haya na yakar kungiyar boko haram a Najeriya, inda suke fada ta kasa da kuma yin amfani da jiragen yaki ta sama.

Fadan dai ya taso ne yayin da gwamanatin Najeriyar ke kokarin cin nasara kafin zaben shugaban kasa da ‘yan majalisun kasar a kar shen wannan watan.

Jami’an gwamnatin Najeriyar sun tabbatar da kasancewar sojin kasashen wajen amma sunce masu bada shawara ne ta bangaren makaman da kasar ta saya daga kasar Afirka ta Kudu, Rasha da kuma Ukrain.

A wata hira da muryar Amurka ranar larabar da ta gabata, shugaba Goodluck Jonathan ya fadi cewar ‘yan kasar wajen kwararru ne aka kawo masu kula da kuma bada horo.

Amma sojin Najeriya sun musanta hakan kamar yadda suka fada wa Muryar Amurka ranar Ralara da ta gabata cewar sojojin kasar wajen ba masu bada shawara bane kawai, da yawan sun a kasancewa a filin daga.

Yanke shawarar kawo kawo sojoji ‘yan kwangila masu zaman kansu a wannan fadan abu ne mai sarkakiya ga gwamnatin Goodluck wanda yake fuskantar kalubale da ga abokin takarar sa Muhammadu Buhari.

A yayin da gwamnatin kasar ta amince wa sojin Jamhuriyar Nijar da na Chadi shiga cikin kasar domin fada da ‘yan kungiyar ta boko haram, kasancewar soji wajen yankin – Afirka ta kudu ko kuma gabacin turai ya kawo babbar tambaya a dangane da tasirin gwamnatin ta Jonathan wajan yaki da ‘yan kungiyra sa kan.

Kungiyar boko haram mai tada kayar baya da zubda jinni ta hallaka dubban jama’a da kuma raba fiye da miliyan guda da muhallan su a arewacin Najerya.

Wani daga cikin sojojin da ke tare da sojin kasar wajen a wani bariki da ke cikin garin Maiduguri ya gano cewar bakin sojojin dai ‘yan kasar Afirka da ukrain da kuma wasu. Ya kara da cewa suna tashi da jiragen sama daga filin jirgin Maiduguri.

“Afirka ta kudu bata son tura sojin ta zuwa tare da mayakan na Najeriya suna son zuwa dan kansu ne” a cewar wani saja wanda ba’a bashi izinin yin magana da kafar watsa labarai ya fada wa muryar Amurka.

Wani kofur na soja kuma ya fada wa muryar Amurka cewar sojin Najriya da na kasashen wajen na nan na shawagi kusa da garin Bama a farkon satin nan.

Amma rashin fahimtar sadarwa ya faru zakanin sojojin Najeriya inda sukayi tsammanin masu sarrafa motocin biyu wadanda “sojojine turawa” ‘yan kungiyar boko haram ne. A cewar sojan an kashe matukin guda kafin aka janye kai harin.

A farkon satin nan rohotannni sun fadi cewa an kashe wani soja mai zaman kanshi dan kasar Afirka ta kudu wanda ke aiki a matsayin dan kwangila a arewa maso gabas amma bau tabbacin cewa ko mutawar tashi ta faru a wannan lokacin ne.

Wakilin huddar kasa da kasa na Afirka ta kudu kan hadin kai bai ce komi akan rahoton.

“sojojin fararen fata sukadai ne suka san yadda ake sarrafa rokokin da ake harbawa da na’urar hannu” a cewar wani kofur.

Kofur din wanda ke zama a barikin sojin na Maiduguri ya ce ‘yan Afirka ta kudun suna tuka jiragen yakin sojojin na Najeriya. Jiragen sintiri da masu saukar ungulu da kuma duk na Afirka ta kudu ne.

“Duk harin da ake kaiwa ta sama farar fatar ne ke kaiwa ta wajan anfani da jiragen da Najeriya tayo har su.

Wani jami’in da ya kasan ce mataimakin kwamandar rundunar tsaro a Borno ya fada ma muryar Amurka cewa akwai kimanin sojin kasar waje 100 zuwa 150, yawanci ‘yan Afirka ta kudu kuma suna aiki cikin Maiduguri ta jirgen yaki.

A ranar 27, na fabarairu wakilin Muryar Amurka ya gani da idonsa wani jerin motocin yaki masu sulke na kan tafiya arewa akan babbar hanya tsakani babban birnin kasar Abuja da Maiduguri.

Matukan fararen fata ne amma mafi yawan mutanen da ke bayan motar bakaken fata ne, kuma wasu daga cikin dogayen motocin suna dauke da tutocin Najeriya.

Batun Zaben

Shugaba Jonathan na fuskantar babban kalubale a zabe mai zuwa yayin da zai yi takara da Janar Muhammadu Buhari, wanda tsohon soja ne da ya taba shugabantar kasar a lokacin mulkin soja.

Da farko an yi niyyar gudanar da zaben ne a watan da ya gabata, sai dai rashin dakile barazanar hare-haren Boko Haram ya sa hukumar zaben ta matsar da shi zuwa ranar 28 ga watan Maris.

A ‘yan makwannin nan, gwamnatin kasar na ikrarin samun galaba akan mayakan. Kasashe makwabta irinsu Chadi da Kamaru da Nijar sun taimaka a fadan inda suka dinga kai hare-hare a sansanonin mayakan a Najeriya.

Ganawa da Jonathan

A ranar Alhamis a Abuja, wani jami’in gwamnatin Najeriya, wanda ya ce kada a bayyana sunansa, ya gayawa VOA cewa Najeriya ta sayo sabbin tankunan yaki da dogayen motoci da kuma kayayyakin gina gadoji da kuma jiragen sama na yaki, inda ya ce dakarun kasar waje sun shiga Maiduguri kuma dauke da makamai.

“Yanzu muna da wadannan kwararru, sun kware a fannin horarwa, wadanda kuma za su horar da mutanen mu su kuma kula da makaman mu.” Jonathan ya ce a wata hira da aka watsa a VOA a ranar larabar da ta gabata.

A cewar jakadan Afrika ta Kudu a Najeriya, Lulu Mnguni, ba shi da wata masaniya game da cewa kasarsa ta sayarwa da Najeriya makamai, amma ya ce a baya akwai cinikayyara makamai tsakanin kasashen biyu.

A watan Janairu, Ministan harkokin tsaron Afrika ta Kudu, ya ce idan har sojojin haya ko na kwantiragi masu zaman kansu za su je Najeriya, za a hukunta su a karkashin dokar Afrika ta Kudu idan suka koma gida.

Shi ma a nashi tsokacin, David Zounmenou, wanda babba ne a fagen bincike a wata cibiya da ta kware a fannin horar wa akan tsaro, tun da har Najeriya ta kai ga hayan jami’an tsaro masu zaman kansu, a kuma mataki na ba da horo, hakan na nuna karara matsalar shigar dakarun wata kasa cikin Najeriyar.

“Ina ga yafi sirri idan aka dauki hayan jami’an tsaro masu zaman kansu domin su gudanar da aiki, maimakon a saka wani jami’i da zai kawo sarkakiya ta fuskar siyasa yayin da ake fuskantar zabe.” Zounmenou ya ce.

Sai dai ya yi gargadin cewa hakan zai iya haifar da zaman doya da manja tsakanin shugaba Jonathan da dakarun kasarsa.

“Akwai wasu kawararru a bangaren dakarun Najeriya, idan aka basu dama da abin da ya dace, za su iya aikin, a gani na, akwai kwararru har yanzu a rundunar sojin Najeriya. Idan har aka kawar da su gefe aka kawo bakin sojoji daga wata kasa, ina ganin hakan ba zai musu dadi ba.” Zounmenou ya jaddada.

Tun daga shekarar 2009, batun matsalar tsaro ta zama wani abu mai kama da yakin sunkuru inda ‘yan kunar bakin wake ke kai hare-hare tare da kaiwa sojoji hari su tsere.

Kungiyoyin fararen hula da masu fafutuka, sun jima suna zargin sojojin Najeriya da laifin rura wutar take hakkokin bil adama da ya dabaibaye arewa maso gabashin kasar.

A bara, VOA ta samu wasu hujjoji da su ka nuna yadda sojojin ke kashe wasu da ake zargin suna nuna goyon baya ga ‘yan kungiyar Boko Haram.

XS
SM
MD
LG