Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

CAN ta ce Bata san da Batun Kudi Naira Biliyan 7 na Kemfe ba


Shugaban kungiyar Kristoci shiyar arewa maso gabas, Rabaran Dr. Shu’aibu Bel, ya gargadi ‘yan siyasa da su daina kalaman da zasu tada hankali ga magoya baya, su kuma daina gwamutsa siyasa da addini.

Rabaran Shu’aibu Bel yayi wannan jawabi ne a jihar Bauchi a karshen taron shekar-shekara na kungiyar. Ya kuma nisanta kungiyar da batun kudi naira biliyan bakwai da wani shugaban krista yace an ba kungiyar Kristocin Najeriya.

Rabaran Bel ya yi kira da ‘yan siyasa su daina yin kalaman batanci da na zarge-zarge, amma su nemi kuri’a da kuma bayyana abinda zasu yi in an zabe su. In kuma ba a zabe su ba, su gaya wa mutane cewa zasu yi tafiya da duk wanda yayi nasara shi ya fi dacewa.

Rabaran kuma ya karyata batun da aka ce an ba kungiyar CAN kudi, kuma yace ba za su yarda da duk wani abu da zai kawo tashin hankali ba ko rarrabe-rarrabe tsakaninsu ba.

Shi ma malam Mohammed Tasi’u Pantami, Kwadinatan kungiyar Arewa Citizen Actin for Change, cewa yayi addini dabam, siyasa dabam.

“sau da yawa sai ka ga ana fakewa da addini a lokacin siyasa haka kuma akan fake da siyasa a shiga harkar addini, shi ya sa muke so mu wayar wa mutane da kai akan cewa kada su gwamutsa siyasa da addini, musamman wadanda ke cikin karkara da kananan hukumomi wadanda ake amfani da su saboda karancin wayewar al’amuran siyasa da na addini da suke da shi”, a ta bakin Malam Tasi’u.

Mai bishara Musa Misal, shugaban hadakar kungiyar Musulmi da Kristoci kuma, yace irin kalaman da ‘yan siyasa ke amfani da su lokacin yakin neman zabe zai iya kawo rikici. “Yawancin lokuta sai dai su dinga fadin yadda zasu ci zabe da kuma yi wa juna gugar zana, galibin su ba sa ma maganar a zauna lafiya wanda kuma wannan sabanin yarjejeniyar da suka yi ce da magoya baya” inji Musa mai bishara.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG