Yayin da zaben Najeriya ke karatowa kungiyoyi da dama na cigaba da fadakar da jama'a akan mahimmancin zaman lafiya lokacin zabe da ma bayan an gama.
Wata kungiya karkashin Farfesa Ibrahim Gambari, ta kai ziyara jihar Naija da nufin fadakar da mutane su gudanar da zabukan da za'a yi ba tare da zubar da jini ba.
Kungiyar ta gana da gwamnan jihar Dr. Muazu Babangida Aliyu wanda kuma shi ne shugaban gwamnonin arewa goma sha tara.
Farfesa Gambari ya ce kungiyar ta samo asali ne daga Abuja to amma domin kasar na da fadi suka yi shawarar su zagaya su fadakar da jama'a domin su gudanar da zabukan cikin kwanciyar hankali ba tare da zub da jini ba.
Bishop Idowu Fearon wanda ya ke cikin tawagar ta Farfesa Gambari ya ce suna jihar ne su ga gwamnan domin ya mika sakonsu ga sauran gwamnonin arewa.
Ya kara da cewa basa son tashin hankali a zabe mai zuwa ya na mai cewa a zaben 2011 babu bangaren Najeriya da ya sha wuya kamar bangaren arewa.
Shi ma gwamnan Naija ya yaba da tawagar da kokarin da ta ke yi inda ya ce ya na son a tunawa mutane cewa akwai rayuwa bayan zabe saboda haka duk wanda ya kai kansa aka kashe ya san babu zabe a ranar lahira.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.