Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: An Kama Wani da Ya yi Aringizon Katunan Zabe


Mutane su na kada kuri'unsu a Najeriya
Mutane su na kada kuri'unsu a Najeriya

A Najeriya ana ci gaba da samun mutane dauke da katunan zabe da dama yayin da kasar ke tunkarar zabuka nan da wasu 'yan makwanni.

Sojoji sun cafke wani da ya boye katunan zabe masu dimbin yawa.

Bobi Kwatare shi ne wanda aka kama da katunan zabe kusan tamanin da uku a jihar Adamawa bayan da ya shiga hannun 'yan sanda a wurin da ake binciken ababan hawa.

A cewar sa wani jami'in gunduma ne ya bashi katunan ya rabawa wadanda suke gudun hijira a kan duwatsu.

Yanzu haka sojojin sun mikashi hannun rundunar 'yan sandan jihar Adamawa domin su ci gaba da bincike.

Rundunar 'yan sandan jihar ta Adamawa ta tabbatar da aukuwar lamarin.

A cewar 'yan sandan, wanda aka kaman ya ce ya zo ganin kishiyar mahaifiyarsa ne sai jami'in ya bashi katunan zaben ya ba wadanda suke kan duwatsu domin a cewarsa babu kafar sadarwa a inda su ke.

To saidai hukumar zabe ta ce ba da yawun ta aka yi badakalar ba domin ba ta amince a ba wani katin wani ba saboda dokikin zabe basu amince da hakan ba.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:23 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG