Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyun Bangaren PDP Ke Neman a Dage Zabe - In ji APC


Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyar APC, Janar Muhammadu Buhari, ya na jawabi a wajen WANI taron manema labarai.
Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyar APC, Janar Muhammadu Buhari, ya na jawabi a wajen WANI taron manema labarai.

Babbar jami'yar adawa ta APC ta ce wasu jami'yyu da ke goyon bayan jam'iyar PDP ne ke yunkurin su ga an sake dage zabe.

Jam'iyyar APC ta ce jam'iyyun sun kai su 12 da ke bangaren jam'iyyar PDP wadanda su ka nace sai a dage zaben.

Ta kara da cewa PDP ba ta son a yi amfani da na'urar da ke tantance mutane, wato Card Reader domin ta shahara a wurin yin magudin zabe.

Kyftin Muhammad Bala Jibril na jam'iyyar APC ya ce suna da hujjoji da za su dogara a kai cewa wadanda ba sa son a yi zabe PDP suke yi wa aiki.

Ya ce dama sun sha fada cewa ita jam'iyyar PDP ta na da wasu jam'iyyu da suka kai 13 duk nata ne suna kuma cikin aljihunta.

Jam'iyyu 12 da suka ruga kotu ba su ba da mamaki ba domin sabili da hakan aka kafasu.

Malam Jafar Sani Bello na jam'iyyar PDP ya musanta duk zargin da ake yi masu.

Ya ce wadanda ba su da katabus na yadda za su samu kuri'un 'yan Najeriya ke yin zargin.

Ya ce gwamnatin tarayya da ke karkashin PDP ta ba da kudin sayo naurorin.

"Sabili da haka menene dalilin da zai sa PDP ta ki yadda da yin amfani da naurar." In ji Bello.

Ga dai karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:18 0:00
Shiga Kai Tsaye

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG