Rahotanni daga Najeriya na cewa ‘yan sanda na shirin shiga yajin aiki a ranar 28 ga watan na Maris da za a gudanar da zaben kasar.
‘Yan sandan su na korafin cewa ba a biya su hakkokin su na karin girma da na ajiye aiki ba wanda aka jingine tun shekaru biyu da su ka gabata.
Sai dai Kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriyar, Emmanuel Ojukwu, ya ce wasu “’yan bata gari ne” daga cikin ‘yan sandan su ke zuga kananan su shiga yajin aikin.
Hakan ya sa rundunar ta yi gargadin cewa duk wanda ya shiga yajin aiki za a hukunta sa bisa dokar kasa.
Wannan martini da rundunar ta fitar, ya sa wasu da dama ke ganin akwai kanshin gaskiya game da batun yajin aikin.
Sai dai a bangaren ‘yan siyasar kasar ba haka su ke kallon lamarin ba, domin a cewar bangaren masu adawa, wannan wani yunkuri ne na dage zaben da aka shirya za a yi a ranar ta 28.
“Wannan yaudara ce, ana so a ce ai manyansu ma sun yi musu magana kada su shiga yajin aikin sun bijire, da sanin manyan, domin a ce ba za a yi zabe ba, to tun kafin su kifta ido su ce bisimilla mun gane su.” In ji Injinya Buba Galadima.
Amma wani jami’in ‘yan sanda ya ce bai kamata a zarge su da hakan ba duk da cewa akwai wasu baragurbi a cikinsu.
“‘Yan sandan da aka sani shekaru goma da su ka wuce ba haka su ke yanzu ba, sun san ka’idojin aikin.” In ji wani jami’in ‘yan sanda da ba ya so a ambaci sunansa.