Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za a Sako O.J. Simpson Daga Gidan Yari


Daryo kechib. Hindiston.
Daryo kechib. Hindiston.

Tsohon fitaccen dan wasan kwallon kafa nan na Amurka kuma dan wasan kwaikwayo, O.J. Simpson, ya ce zai koma gida ga iyalansa da abokanansa bayan da wata hukuma da ke yafiya ga fursunoni ta bayyana cewa ta amince a sake shi.

Wata hukumar da ke yin afuwa ga fursunoni a birnin Les Vegas dake jihar Nevada, ta amince za ta saki tsohon shahararren dan wasan kwallon kafa kuma dan wasan kwaikwayon Amurkan nan O.J. Simpson, bisa tsarin nan na afuwa.

Za a sake shi ne bayan da ya kwashe shekaru tara a gidan yari bayan da aka same shi da laifin yin fashi da makami.

An yi wa Simpson mai shekaru 70 afuwa ne bayan da aka ba da rahoton da ya nuna tabbacin cewa ya nuna ladabi da biyayya yayin da yake zaune a gidan yarin.

Tsarin yin afuwa na gudana ne bisa sharadin cewa za a rika lura da halayyar mutumin da aka yi wa afuwa a ga ko zai sake aikata wani laifi.

“Na gode,” in ji Simpson wanda cikin murmushi amma a gajiye ya nuna jin dadinsa bayan da aka bayyana sanarwar.

Ba a dai kwashe wani tsawon lokaci ba a lokacin yanke wannan hukunci inda aka yi zaman cikin kasa da sa’a guda.

“Ina mai ba da hakuri kan yadda wannan abu ya faru,” Simpson ya fadawa hukumar a farkon yinin jiya Alhamis.

A shekarar 2007 aka samu Simpson da laifin yin fashi da makami da yin garkuwa hade da wasu tuhume-tuhume da suka hada da tunkarar wasu mutane biyu da ke sayar da kayan tarihin fitattun ‘yan wasa inda ya yi ikirarin cewa na sa ne aka sace.

An yanke mai hukuncin zaman gidan yari mafi karanci na tsawon shekaru tara maimakon shekaru 33 bayan da aka same shi da laifi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG