Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Jam'iyar Republican suna cizon yatsa da gaza canza tsarin inshorar lafiya


The casket of Rep. John Lewis, a pioneer of the civil rights movement and long-time member of the U.S. House of Representatives, moves over the Edmund Pettus Bridge by horse drawn carriage during a memorial service in Selma, Alabama.
The casket of Rep. John Lewis, a pioneer of the civil rights movement and long-time member of the U.S. House of Representatives, moves over the Edmund Pettus Bridge by horse drawn carriage during a memorial service in Selma, Alabama.

Shugaba Donald Trump da 'yan jam'iyar Republican suna cizon yatsa bayan yunkurinsu na canza tsarin inshora yaci tura.

‘Yan jam’iyar Republican suna cizon yatsa, biyo bayan gaza cimma burinsu na rage sa hannun gwamnati a tsarin inshorar kiwon lafiya, da ya bada damar ci gaba da amfani da dokar kiwon lafiya ta tsohon shugaban kasar Barack Obama da ake kira Obamacare.
Kasa samun goyon bayan kafa dokar kiwon lafiyar da ‘yan jam’iyar Republican suka yi, wani babban koma baya ne ga shugaba Donald Trump, da ya kuma karawa ‘yan jam’iyar Democrat marasa rinjaye karfin guiwa.
Shugaban 'yan Republican masu rinjaye a majalisar dattijai, Mitch McConnell, ya bayyana wannan koma baya, bayanda ‘yan jam’iyar guda biyu suka yi watsi da kudurin.

‘Yan jam’iyar Republican sun gabatar da wata shawarar soke tsarin inshora na Obamacare ba tare da maye gurbinta ba baki daya. Nan da nan sanatoci ‘yan jam’iyar Republican suka nuna rashin goyon bayan wannan shawarar, kamar yadda ‘yan jam’iyar Democrat suka yi.

Trump ya yi alkawarin jam’iyar Republican zata sami nasara a wadansu batutuwa masu muhimmanci kamar, yiwa tsarin haraji garambawul, sai dai masu kula da lamura suna cewa, zai kara zama mawuyaci kasancewa, ‘yan jam’iyar Republican sun sami rauni, yayinda tauraron shugaba Trump yake dishewa bayan koma bayan da ya samu a batun tsarin kiwon lafiyar.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG