Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Yaba Da Takunkumin Da Aka Kakabawa Wasu Manyan Sojin Syria


Amurka ta yaba ma kungiyar Tarayyar Turai saboda kakaba takunkumin da ta yi yiwa wasu manyan jami'an sojin kasar Siriya da wasu masu ilimin kimiyyar kasar jiya litini wadanda ke da hannu a harin makaman da aka kai kan farar hula.

Matakan hadin gwiwa na Amurka da kungiyar Tarayyar Turai, wani bangare ne na hobbasar da ake yi a matakin kasa da kasa na ladabtar da gwamnatin Assad saboda saba ma dadaddiyar ka'idar kasa da kasa ta hana amfani da makamai masu guba," a cewar mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka, Heather Nauert.

Jami'ai 16 da aka kakaba ma takunkumin an hana su shiga Turai, kuma za a kwace kaddarorinsu da ke Turai.

Ministan Harkokin Wajen Burtaniya, ya bayyana matakin da kungiyar ta EU ta dauka jiya Litini a matsayin mataki mai kyau sannan ya kara da cewa ya yi farin cikin ganin Ministocin sun hada kai wajen maida hankali kan wannan batun.

Majalisar dinkin duniya da Hukumar Hana Amfani da makamai masu guba na gudanar da bincike na bai daya kan harin da aka kai a watan Afirilu da iskar sarin a Khan Sheikhun da ke Siriya, wanda da hallaka mutane akalla 87.

A hotunan bidiyon harin har akwai inda ke nuna yara na fitar da kumfa ta baka, kuma su na numfashi da kyar.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG