Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan sandan Da Suka Harbe Wata Mata a Amurka Sun Ce Sun Razana Ne


'Yan sanda suna tsare masu zanga zanga yayin wani boren nuna kin jinin 'yan sanda saboda harbin mutane da suke yi a Amurka
'Yan sanda suna tsare masu zanga zanga yayin wani boren nuna kin jinin 'yan sanda saboda harbin mutane da suke yi a Amurka

Hukumar dake binciken harbe wata mata ‘yar Australia har lahira da ‘yan sanda suka yi a Minneapolis dake jihar Minnesota, ta ce daya daga cikin jami’an 'yan sandan ya ce ya razana ne da wani kara da ya ji, jim kadan kafin abokin aikinsa ya yi harbe matar wacce ba ta dauke da makami.

A ranar Asabar din da ta gabata 'yan sanda suka kashe Justine Damond a wani lungu, wacce malamar koyar da ilimin zurfin tunani ce, wacce kuma ke shirin amarcewa.

An harbe ta ne a bayan gidanta bayan da ta kira lambar gaggawa ta neman dauki a lokacin da ta gabatar da rahoton da ya nuna alamun wani na son ya yi mata fyade.

A wata hira da aka yi da dan sandan dake tuka motar da ta kawo dauki a ofishin hukumar binciken manyan laifuka ta Minnesota, Matthew Harrity, ya ce Damond ta tunkarin motarsu ne bayan da wani kara ya razana shi, lamarin da ya sa abokin aikinsa, Mohamed Noor, ya harbe matar wacce ba ta dauke da makami daga inda yake zaune.

Rahotannin su ce nan take ‘yan sanda biyu suka dauki matakin bai wa matar agajin gaggawa kafin motar daukan marasa lafiya ta iso wurin.

Sai dai nan take a wurin Damond mai shekaru 40, wacce ‘yar asalin birnin Sydney ce a Australia ta cika.

Jami’an tsaran sun ce na’urar daukan hoton dake jikin Noor a kashe take, wanda hakan ya sabawa dokar aikin dan sanda a Minneapolis.

Yanzu haka ‘yan sanda biyu na zaman hutun dole a gida amma ba tare da wani abu ya shafi albashinsu ba.

Matsalar 'yan sanda su harbe mutum har lahira, ba bakon abu bane a Amurka, inda a lokuta da dama sukan yi ikirarin cewa suna hakan ne a kokarin kare kansu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG