Fadar shugaban Amurka ta ki ta bada cikakken bayani akan ganawar da shugaba Donald Trump yayi da shugaban Rasha Vladimir Putin a lokacin taron kungiyar kasashen G-20 da aka yi cikin farkon watan nan.
Wata mai magana da yawun fadar shugaban Amurka Sarah Huckabee Sanders ta fadawa manema labarai da suka tiso ta gaba jiya Laraba da tambayoyi akan batutuwan da shugabannin suka tattauna, cewa liyafa ce ta hutawa saboda lokacin hutu ne a yammacin.
Sanders ta ce idan akayi la’akari da rahotannin ganawar Trump da Putin kwana daya kafin ganawar, karon farko da Amurka ta sami wannan bayanin, “shirme ne a bayyana ganawar shugabannin a matsayin kebabbiya, bayan sauran shugabannin kasashe fiye da 10 da masu yin fassara na zaune kusa da su kuma kowa na ganin su a lokacin wannan liyafar da aka yi a wani makeken dakin cin abinci.”
Duk da haka, a jiya Laraba, a lokacin da aka yi masu tambaya akan ganawar Trump da Putin karo na biyu a wurin taron, tsofaffin jami’an diplomasiyya da yawa, da kwararru a harkokin siyasa, da ‘yan majalissa daga jam’iyyar Democrat sun sha nanata cewa “da walaki”, wannan “ba abinda aka saba gani bane.”
Facebook Forum