Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Kolin Kwango ta tabbatar da nasar Kabila a zabe


Tashin hankalin bayan zaben Kwango.
Tashin hankalin bayan zaben Kwango.

Kotun Kolin Janhuriyar Dimokaradiyyar Kwango ta tabbatar da nasarar Shugaba

Kotun Kolin Janhuriyar Dimokaradiyyar Kwango ta tabbatar da nasarar Shugaba Joseph Kabila a zaben da aka gudanar.

Kotun ta sanar jiya Jumma’a cewa Mr. Kabila ya sami kusan 49% na kuri’un da aka kada a watan Nuwamba, kuma wai bangaren adawar ya kasa kafa ingantattun hujjoji kan zarge-zargen magudin da ya ce an yi a zaben.

Tunda farko a jiya Jumma’ar Shugabannin Kungiyar Yankin Great Lakes na Nahiyar Afirka sun yi na’am da sake zaben Shugaba Kabila dukko da takaddamar.

Mambobin Kungiyar Ganawar Kasa da Kasa kan yankunan manyan tabkuna sun bayar da wata takardar bayanin bayan taro a karshen taron nasu na kwana biyu a Kampala, babban birni Uganda inda a ciki su ke taya Mr. Kabila kan nasarar da ya yi. Kungiyar ta kuma yi kira ga jam’iyyun adawar da su ka kalubalanci sakamakon da su yi na’am da shi su kuma dukufa kan gina kasar ta Kwango.

Masu sa kula da zaben na kasa da kasa dai sun ba da rahotannin magudi sosai a lokacin kada kuri’a da kuma lokacin kidaya.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG